A ranar Laraba ne wasu jiga-jigan ‘yan siyasa a Nijeriya suka kafa ƙawancen haɗaka ta tunkarar Jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar a zaɓen shekarar 2027.
Haɗakar, wadda ta zaɓi jam’iyyar ADC a matsayin inda za ta dunƙule domin zaɓen shekarar 2027, ta ƙunshi sanannun ‘yan siyasa daga faɗin Nijeriya.
Ga wasu daga cikin sanannun ‘yan siyasar da suke cikin ƙawancen ‘yan hamayyar da suka halarci bikin bayyana haɗakar a Abuja.
David Mark
David Mark tsohon shugaban majalisar dattawan Nijeriya ne, wanda ya riƙe muƙamin tun shekarar 2007 zuwa shekarar 2015.
Shi ne aka ayyana a matsayin shugaban Jam’iyyar ADC a wajen taron haɗakar da aka yi ranar Laraba a ɗakin taro na ‘Yar’adua Center da ke Abuja.
A ranar Talatar da ta gabata ne David Mark ya fice daga Jam’iyyar PDP bayan ya shafe shekara 27 yana cikin Jam’iyyar da ta yi mulkin ƙasar daga shekarar 1999 zuwa shekarar 2015.
David Mark, wanda ya taɓa riƙe muƙamin Ministan Sadarwa a lokacin mulkin soja, ya fito ne daga Jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar ƙasar.
Rauf Aregbesola
Rauf Aregbesola shi ne aka naɗa a matsayin sakatare na wucin-gadi na Jam’iyyar ADC a taron haɗakar ‘yan adawar.
Aregbesola ya fito daga jihar Osun a kudu maso yammacin Nijeriya, amma ya yi kwamishinan ayyuka a jihar Legas a lokacin gwamna Bola Ahmed Tinubu.
Bayan wannan ne ya zama gwamna a jihar Osun a ƙarƙashin jam’iyyar inda ya shafe shekara takwas yana mulki a jihar.
Aregbesola yana cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar APC a shekarar 2014 kuma ya yi Ministan Tsaron Cikin Gida a lokacin mulkin Buhari daga shekarar 2019 zuwa shekarar 2023.
Atiku Abubakar
Atiku Abubakar shi ne mataimakin shugaban Nijeriya daga shekarar 1999 zuwa shekarar 2007.
Kafin ya yi Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abukakar, wanda ya fito daga jihar Adamawa a arewa maso gabashin Nijeriya, ya yi aiki da hukumar kwastam.
Atiku Abubakar na cikin waɗanda suka shiga zaɓen fitar da gwani na zaɓukan 1993.
Kuma tun shekarar 2007 yake neman shugabancin Nijeriya. A halin yanzu Atiku Abubakar na cikin jiga-jigan ‘yan hamayya da suke cikin haɗakar ADC.
Peter Obi
Peter Obi wanda ya fito daga jihar Anambra, shi ma yana cikin jiga-jigan ‘yan siyasar da suke cikin haɗakar ‘yan hamayyar.
Peter Obi ya yi gwamnan jihar Anambra daga shekarar 2007 zuwa 2014.
Kuma a shekarar 2023 ya yi takarar neman shugaban ƙasar Nijeriya a ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar Labour Party.
Nasiru Ahmad el-Rufai
Nasiru Ahmad El-Rufai ya shi ma jigo ne a cikin ‘yan siyasar da suka haɗu a jam’iyyar ADC.
Ɗan siyasar, wanda ya fito daga jihar Kaduna a arewa maso yammacin Nijeriya, ya yi Ministan Birnin Tarayya Abuja a ƙarƙashin mulkin Obasanjo daga shekarar 2003 zuwa 2007.
Yana cikin ‘yan siyasar da suka kafa jam’iyyar APC, kuma ya yi gwamnan jihar Kaduna daga shekarar 2015 zuwa shekarar 2023.
Yana cikin ministocin da aka kai sunayensu majalisar dokokin Nijeriya domin tantancewa a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, amma ba a tantance shi ba.
Abubakar Malami
Abubakar Malami, wanda ya fito daga jihar Kebbi, yana cikin ‘yan siyasar da suka kafa Jam’iyyar APC.
Ya riƙe mukamin Babban Lauyan Nijeriya a ƙarƙashin gwamnatin Buhari daga shekarar 2015 zuwa 2023.
Kuma yana cikin jiga-jigan ‘yan siyasar da suka kafa hadakar ‘yan hamayya ta ADC.
Chibuike Rotimi Amaechi
Chibuike Rotimi Amaechi, wanda ya fito daga jihar Ribas da ke kudu masu kudancin Nijeriya, yana cikin haɗakar ‘yan hamayyar da suka shiga ADC.
Amaechi ya yi shugaban majalisar dokokin jihar Ribas kafin ya yi gwamnan jihar na tsawon shekaru takwas.
Kazalika yana cikin ‘yan siyasar da suka kafa jam’iyyar APC a shekarar 2013, kuma bayan Buhari ya ci zaɓe a shekarar 2015 an ba shi Ministan Sufuri, muƙamin da ya yi daga shekarar 2015 zuwa 2023.
Solomon Dalong
Solomon Daluong, wanda ya fito daga jihar Filato da ke tsakiyar Nijeriya, tsohon ma’aikacin hukumar gidan gyara hali na Nijeriya ne.
Ya kasance ɗan jam’iyyar APC a ƙarƙashin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari inda ya yi aiki a matsayin Ministan Matasa da Wasanni daga shekarar 2015 zuwa 2019.
Sai dai yanzu shi ma yana cikin haɗakar ‘yan siyasar da suke neman a tunkari jam’iyyar APC a ƙarƙshin inuwar jam’iyyar ADC.
Aminu Waziri Tambuwal
Aminu Waziri Tambuwal, da ya fito ne daga jihar Sokoto a arewa maso gabashin Nijeriya, ya yi shugaban majalisar wakilan Nijeriya daga shekarar 2011 zuwa 2015.
Kazalika ya yi gwamnan jiharsa ta Sokoto daga shekarar 2015 zuwa 2023.
Yana cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar APC. Sai dai daga baya ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar PDP.
A halin yanzu kuma yana daga cikin jiga-jigan jam’iyyar ADC.
Sadique Abubakar
Sadique Abubakar tsohon hafsan sojin saman Nijeriya ne kuma ya shiga jam’iyyar APC inda ya yi takarar gwamnan jiharsa ta Bauchi da ke arewa maso gabashin Nijeriya a shekarar 2023.
Sai dai kuma bai yi nasara ba a takarar bayan da Bala Mohammed na jam’iyyar PDP ya kada shi.
Har wa yau, Sadique Abubakar yana cikin ‘yan siyasar da suka shiga haɗakar ADC da aka ayyana ranar Laraba.
Emeke Ihedioha
Emeke Ihedioha ya yi Matakaimakin Shugaban Majalisar Wakilan Nijeriya daga shekarar 2011 zuwa shekarar 2015.
Kazalika ya yi gwamnan jiharsa ta Imo tsawon shekara ɗaya kafin shari’ar kotu ta karɓe ragamar mulkin.
Dino Melaye
Dino Melaye ya fito ne daga jihar Kogi a arewa maso tsakiyar Nijeriya, kuma yan cikin ‘yan siyasar da suka kafa jam’iyyar APC.
Ya yi sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma a Majalisar Dattawan Nijeriya daga shekarar 2015 zuwa 2019.
Ya yi takarar gwamnan jiharsa ta Kogi a shekarar 2019 da kuma 2023, amma bai yi nasara ba.


















