AFCON 2025: Osimhen da Mane sun ci ƙwallo, yayin da Nijeriya ta yi nasara, Senegal ta yi kunnen doki
Nijeriya ta ci Tunisiya 3-2 inda ta samu gurbin shiga zagaye na biyu na ƙasashe 16.
Manyan 'yanwasan gaba Victor Osimhen da Sadio Mané sun zura ƙwallaye a daren Lahadi yayin da Nijeriya ta samu shiga zagayen sili-ɗaya-ƙwale a gasar Cin Kofin Afirka AFCON a Maroko, Senegal kuma ta ta fara jin ƙanshin shiga zagayen na gaba.
Osimhen ne ya buɗe wa Super Eagles ƙofar zura ƙwallaye kafin hutun rabin lokaci, kuma suka ƙara tazarar kwallayen zuwa uku kafin su tsira daga matsin lambar Tunisia a ƙarshen wasan, inda aka tashi Nijeriya ta yi nasara da 3-2 a Fas.
Wannan nasara ta tabbatar da cewa Nijeriya, wacce ta ke da kofuna uku, ta zama ƙasa ta biyu bayan Masar, mai tarihin lashe kofin sau bakwai, da ta samu gurbi a zagaye na ‘yan 16.
Mané ya zura kwallo yayin da Senegal ta rama cin da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ta yi muta a Tangier, inda aka tashi 1-1, sakamakon da ya sa dukkan tsoffin zakarun na Afirka suka kama hanyar zuwa zagaye na biyu.
Osimhen ya kasance barazana ga 'yan Tunisiya yayin da ya zura kwallonsa a biyu a AFCON, kuma ta farko tun daga zagaye na farko a gasar ta 2024.
Uganda da Tanzania cikin rashin tabbas
Nijeriya, wacce ta inganta wasanta sosai bayan nasarar da ta samu da ƙyar a wasant na farko daTanzania, kasar, ta rasa kuzari a karshen wasan kuma Tunisia sau biyu tana yunƙurin rama duka ƙwallayen da aka zura mata, a daidai sa’ar da aka yi ƙarin lokacin kafin a tashi.
Kyaptin Wilfred Ndidi, wanda ya zura kwallo ta farko a tawagar ƙasa, da Ademola Lookman sune sauran 'yan Nijeriya da suka zura ƙwallo, kafin Montassar Talbi da Ali Abdi su rama, abin da ya sanya wasan ya yi zafi daga ƙarshe.
Nijeriya na da maki shida a Rukunin C, Tunisia uku, yayin da Tanzania da Uganda ke da maki daya kowannensu kafin zagayen karshe na wasanni ranar Talata.
Allan Okello na Uganda ya kasa cin bugun daga kai sai mai tsaron gida, abin da ya sa tawagarsa ya yi canjaras na 1-1 da makwabtansu Tanzania.
Uche Ikpeazu ya zura ƙwallon da ya farkewa ƙasarsa a karshen wasan a gaban magoya baya 10,540 a Filin wasa Al Medina a Rabat.
‘Sakamako mai ba da haushi’
Kafin haka ana ganin kamar Tanzania, wadda ba ta samu nasara ba a cikin wasanni goma da suka gabata a cikin gasa AFCON huɗu, za ta iya kafa sabon tarihi lokacin da Simon Msuva ya ci ƙwallo a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
A Tangier, Cedric Bakambu ya samareawa DR Congo nasara bayan awa guda da fara wasa, amma ɗanwasan gaba na Al Nassr Mané ya farke ba da jimawa ba, kuma sakamakon ya tabbatar da Senegal na kan gaba saboda bambancin ƙwallaye fiye da sauran, a lokacin da ya rage a buga wasa ɗaya a matakin rukuni.
'Sakamakon ya kasance abin takaici kaɗan. Ya kamata a ce mun ci ƙwallonmu kafin hutun rabin lokaci, amma ba mu yi ba,' in ji kocin Senegal Pape Thiaw.
'Abin da na yaba da shi shi ne himmar da 'yanwasa suka nuna bayan an ci mu kwallo — hakan abu ne mai kyau. Zuwa gaba, dole mu san yadda za mu samu nasara da wuri.'
'Zamu ci gaba da aiki kan yadda za mu mayar da damar mu zuwa ƙwallaye.'
Kocin DR Congo Sebastien Desabre ya ce: 'Mun buga wasan da ya dace mu buga don mu yi gogayya da mafi kyawun ƙungiya a Afirka.
'Na buƙaci 'yanwasa su kasance tare a dukkan sassan wasa, ko a kai hari ko a tsaron gida. N gamsu cewa hakan suka yi.'