Gabannin tattaunawa da Amurka a Oman, Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana a ranar Jumma’a cewa Tehran ta shiga harkar diflomasiyyar ne “da kyakkyawar niyya,” yana mai cewa “ana buƙatar a cika alƙawurra.”
"Iran ta shiga harkar diflomasiyyar da buɗaɗɗen idanu da kuma tunawa da shekarar da ta gabata. Muna tattaunawa da kyakkyawar niyya kuma muna tsaye tsayin daka bisa ‘yancinmu," kamar yadda Abbas Araghchi ya bayyana a wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na X.
"Dole a cika alƙawurra," in ji shi, yana mai jaddada cewa kasancewa a mataki ɗaya da mutunta juna da kuma manufa ɗaya “ginshiƙai ne masu muhimmanci ga yarjejeniya mai ɗorewa.”
An shirya tattaunawa game da shirin nukiliya tsakanin Washington da Tehran a Oman ranar Jumma’a.
Surukin Shugaban Amurka Donald Trump Jared Kushner da kuma manzon Amurka na musamman Steve Witkoff za su wakilci ɓangaren Amurka.
Iran za ta samu wakilcin jami’an diflomasiyya a ƙarƙashin jagorancin Araghchi. Ministan Harkokin Wajen Iran ya isa babban birnin Oman Muscat domin halartar zaman, in ji kamfanin dillancin labaran Tasnim News Agency wanda gwamnatin ƙasar ke da ƙwarƙwaryar iko a kai.















