| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Shugaban Nijeriya Tinubu na neman sake aro dala biliyan 6 daga UAE da Birtaniya
Tinubu ya roƙi Majalisar Dattawa da ta yi “gaggawar amincewa,” yana mai cewa za a jingina rancen da takardun kudi na naira a matsayin kariya.
Shugaban Nijeriya Tinubu na neman sake aro dala biliyan 6 daga UAE da Birtaniya
Shugaban Nijeriya Tinubu na neman sake aro dala biliyan 6 daga UAE da Birtaniya / Reuters
12 awanni baya

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya nemi amincewar Majalisar Dattawa domin karɓar sabbin rance na waje da suka kai dala biliyan 6, domin tallafa wa ayyukan gine-gine da biyan basussuka, da kuma gyaran tashoshin jiragen ruwa.

A cikin wata wasiƙa da aka aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wadda aka karanta a zaman majalisa na ranar Talata, shugaban ya nemi amincewa da rancen dala biliyan 5 daga bankin First Abu Dhabi Bank.

Idan aka amince, jimillar bashin gwamnatin Nijeriya za ta tashi daga dala biliyan 110.3 zuwa dala biliyan 115.3.

Tinubu ya roƙi Majalisar Dattawa da ta yi “gaggawar amincewa,” yana mai cewa za a jingina rancen da takardun kudi na naira a matsayin kariya.

A wata wasiƙa ta daban, shugaban ya kuma nemi amincewa da ƙarin rancen dala biliyan 1 domin gyara Lagos Port Complex da kuma tashar joragen ruwa ta Tin Can Island Port.

A cewarsa, an shirya wannan rance ne ta hannun Citibank London tare da goyon bayan UK Export Finance, domin zamanantar da inganta manyan tashoshin jiragen ruwa guda biyu, ta yadda za a ƙara inganci, tsaro, da kuma yadda suke aiki gaba ɗaya.

Ya bayyana cewa gyaran zai magance matsalolin gine-gine da suka daɗe suna addabar tashoshin, ya kuma daidaita ayyukansu da ƙa’idojin duniya, tare da tallafa wa bunƙasar tattalin arziki.

Shugaban ya ƙara da cewa rancen zai kasance na tsawon shekaru 14 kafin a kammala biya, ciki har da lokacin shiri na watanni 48, tare da kuɗin samuwa (availability fee) na kashi 1.1 cikin ɗari, da kuma kuɗin inshorar UKEF na kashi 1.07 cikin ɗari.

Dukkanin buƙatun guda biyu an miƙa su ga Kwamitin Majalisar Dattawa kan Lamuni na Cikin Gida da na Waje domin ƙarin nazari, tare da umarnin su dawo da rahoto cikin gaggawa.

Kari a kan kasafin kudi

A hannu guda kuma, Shugaban na Nijeriya ya sake rubuta wata wasiƙa zuwa Majalisar Dokoki ta Ƙasa yana neman a yi gyara a kan Kudirin Kasafin Kuɗi na shekarar 2026, inda ya ba da shawarar ƙara naira tiriliyan 9 domin a mayar da jimillar kasafin daga naira tiriliyan 58.4 zuwa naira tiriliyan 67.4.

An isar da wannan buƙata ne ta cikin wata wasiƙa da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya karanta a zauren majalisar yayin zamanta na ranar Talata.

A cewar Shugaban Ƙasar, wannan gyara da ake so an yi shi ne domin ƙarfafa gaskiya a harkokin kuɗi da kuma tabbatar da aiwatar da manyan shirye-shiryen ƙasa yadda ya kamata.

Ya bayyana manyan manufofi uku da ke bayan wannan buƙata, ciki har da daidaita tare da yin bayanin duk wasu basussukan doka da suka rage daga kasafin kuɗin da suka gabata, domin kauce wa su zama nauyi ga aiwatar da kasafin shekarar 2026.

Rumbun Labarai
Sojojin Nijeriya sun daƙile harin ISWAP, sun kashe ‘yanta’adda 38 a Borno
APC ta kammala babban taronta na ƙasa, Nentawe Yilwatda zai ci gaba da zama shugaban jam'iyyar
Nijeriya ta ƙaddamar da shirin riga-kafin HIV, na allurar Lenacapavir
NCC za ta toshe layukan waya masu alaka da damfara a Nijeriya
Nijeriya ta sassauta dokokin kuɗaden waje, kamfanonin man ƙetare za su iya fitar da duk kuɗaɗensu
'Yanta'addan Lakurawa sun kashe sojoji 11 da ɗansanda a harin kwanton-ɓauna a Jihar Kebbin Nijeriya
Sojojin ruwan Nijeriya sun kama masu tserewa Turai a ɓoye ta jirgin ruwa a Legas
NEMA ta karɓi 'yan Nijeriya 708 da suka maƙale a Jamhuriyar Nijar
Zarge-zargen da hukumar ICPC ke yi wa Nasir El-Rufai
Jami’ar Bayero ta Kano ta kori ɗalibai 171 bisa laifin gabatar da takardun bogi
Kotu ta yi wa tsohon babban akantan Nijeriya ɗaurin shekara 72 a gidan yari kan damfarar N868m
Taron gwamnoni a Legas ne ya hana ni zuwa Bikin Hawan Nasarawa – Gwamnan Kano
Tashin farashin mai a Nijeriya ya yi ƙamari yayin da yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran ya ƙi ƙarewa
Amurka ta tura jirage marasa matuƙa Nijeriya don tattara bayanan sirri kan 'yanta'adda
Sarki Charles ya amince da ‘mummunan’ mulkin mallakar da Birtaniya ta yi wa Nijeriya
Sarki Charles ya karɓi baƙuncin Shugaba Tinubu a ziyara mai tarihi a Birtaniya
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda 61 a Malam Fatori da ke arewa maso gabashin ƙasar
Tinubu ya umarci masu riƙe da muƙaman siyasa da ke son tsayawa takara a zaɓen 2027 su ajiye aiki
Tinubu ya umarci manyan hafsoshin tsaron Nijeriya su koma Maiduguri da zama
Hare-haren ƙunar-baƙin-wake sun kashe mutum aƙalla 23 a birnin Maiduguri na Nijeriya