Hukumar ƙwallon ƙafa ta Sifaniya ta dakatar da buga wasannin Talata na gasannin Copa del Rey da Copa de la Reina, bayan samun labarin rasuwar ɗanwasan ƙungiyar Tenerife, Jesus de Miguel a asibiti ranar Talata.
Ɗanwasan mai shekaru 30 ya rasu ne bayan samun bugun zuciya a ranar Litinin, sakamakon yin mummunan karo da golan ƙungiyar Andorra, Jesus Owono, a wani wasa a Sifaniya.
An haƙura da buga wasan ana 2-2, da minti 7 na ƙarin lokaci, bayan da De Miguel ya zube a ƙasa saboda arangama da golan, wanda ya fito daga ragarsa a guje don kaɗe ƙwallon da aka bugo, amma garin haka ya daki ƙirjin De Miguel da gwiwarsa.
An ɗauke De Miguel a gadon majinyata inda motar asibiti ta garzaya da shi asibiti. Shi kuma gola Owono am ba shi jan kati kai-tsaye.
Tenerife ƙungiya ce da ke buga gasar aji na biyu a Sifaniya, kuma wasan na Litinin ya gudana ne a filin wasa na Heliodoro Rodriguez Lopez, wanda ke garin Santa Cruz de Tenerife, a tsibirin Canary Islands, na Sifaniya.
Sanarwa da ta’aziyya
Ƙungiyar tenerife ta fitar da sanarwa mai cewa, “Muna baƙin cikin da jin ciwo, tare da raɗaɗi a maƙwogwaronmu da kasa yarda da cewa wannan abu ya faru a gaske. Daga CD Tenerife muna sanar da rasuwar Jesus de Miguel Alameda”.
“Babu kalamai da za su kwantar mana da rai, sam babu wani abu da zai ɗauke wannan jimamin da ke lulluɓe mu da baƙin ciki.”
Barcelona da Real Madrid, da ma wasu ƙungiyoyin ƙwallo na Sifaniya sun miƙa saƙon ta’aziyya da girmama mamacin.
Su ma ‘yanwasa kamar Kylian Mbappe na Real Madrid, da Achraf Hakimi na PSG, da toshon ɗanwasan Barcelona, Gerard Pique, wanda shi ne shugaban kulob ɗin Andorra, sun fitar da sanarwar ta’azaiyya.
















