| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Jami'an DSS a Nijeriya sun kama makamai da ake zargi an shiga da su Jihar Sokoto daga Nijar
Hukumar DSS ta ce ta ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda 21, manyan bindigogin PKT guda hudu da harsasai 825, tare da kama wata mata da ake zargi da safarar makaman.
Jami'an DSS a Nijeriya sun kama makamai da ake zargi an shiga da su Jihar Sokoto daga Nijar
Hukumar DSS ta kama makamai masu yawa da aka shigo da su Nijeriya daga Nijar / Others

Hukumar tsaro ta farin kaya ta Nijeriya (DSS) ta kama makamai da alburusai masu yawa da ake zargin an shiga da su ƙasar ta haramtacciyar hanya daga Jamhuriyar Nijar.

Gidan talbijin na gwamnatin Nijeriya, NTA, ya ambato wata sanarwa daga DSS tana cewa an gudanar da aikin ne a Dawakawa da ke Ƙaramar Hukumar Goronyo ta Jihar Sokoto bayan samun bayanan sirri kan waɗanda ake zargi da safar makaman.

Sanarwar ta ce jami'an DSS sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda 21 da manyan bindigogin PKT guda huɗu da harsasai 825.

Ta ƙara da cewa yawan kama masu safarar makamai da DSS ke yi ya tilasta wa ƙungiyoyin masu aikata laifuka sauya dabaru, ciki har da amfani da mata da dabbobi masu ɗaukar kaya, musamman raƙuma.

“Hukumar ta bayar da rahoton ƙaruwar mata da ake amfani da su domin safarar makamai, inda aka kama mata goma sha huɗu daga watan Fabrairun 2025 zuwa watan Nuwamba na 2026 a faɗin jihohi da dama,” in ji sanarwar.

Hakan na zuwa ne ƙasa da kwanaki 70 kafin gudanar da babban zaɓen Nijeriya na shekarar 2027.

Masu AlakaTRT Afrika - Hukumar DSS ta Nijeriya ta ƙwato bindigogi 676 da harsasai 332,000

Kazalika a farkon makon nan, jami'an DSS sun kama wata mata da ake zargin tana safarar makamai mai suna Hafsat Umar a Ƙaramar Hukumar Talata Mafara a Jihar Zamfara.

Rahotanni sun bayyana cewa, an same ta da gurneti guda 12 da bel ɗin harsasai guda biyu.

“Hafsat Umar ita ce mace ta 14 da DSS ta kama bisa zargin safarar makamai tsakanin watan Fabrairun 2025 da Nuwamban 2026,” a cewar majiyar tsaro.

Bayanan sirri sun nuna cewa ta yi tafiya zuwa Jihar Neja domin samo alburusai da za ta kai wa wani jagoran 'yanbindiga da ake zargi, mai suna Saidu Marafa, wanda ke zaune a Kani Kawa, Ƙaramar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara.

Kama masu safarar makamai a jihohi daban-daban

Hukumar DSS ta kama wasu mata da ake zargi da safarar makamai a jihohin Zamfara, Nasarawa, Ebonyi, Taraba, Kaduna da Filato.

A cikin irin waɗannan samame, jami'an hukumar sun kama wata Aisha Mohammed a garin Keffi na Jihar Nasarawa a watan da ya wuce, ana zarginta da safarar makamai da alburusai ta hannun wani dillalin makamai da ake zargi da garkuwa da mutane mai suna Sani.

Jami'an tsaro sun ƙwato harsasai 202 masu girman 7.62mm na bindigar AK-47 da harsasai daga hannunta.

Haka kuma a watan Satumban 2026, jami'an DSS sun bayyana cewa sun kama wasu mata biyu, Chika Aguzie da Blessing Nwamba, a wurare daban-daban a Jihar Ebonyi bisa zargin hannu wajen samar da makamai da abubuwan fashewa ga kwamandojin ƙungiyar Eastern Security Network (ESN) da aka haramta.

An danganta matan da wasu kwamandojin ƙungiyar da suka haɗa da Chinonso Amobi Okafor, wanda aka fi sani da Temple, da wani kwamanda mai suna B44, waɗanda ake zargin suna aiki a Jihar Anambra.

A yayin samamen, jami'an sun ƙwato na'urorin tayar da bama-bamai (IED) 14.

Sannan a watan Agusta, DSS ta kama Rabiatu Halidu a kan titin Abacha da ke Ƙaramar Hukumar Katu ta Jihar Nasarawa, ɗauke da harsasai 501 masu girman 7.62mm.

Haka kuma, a watan Fabrairu, an kama wata Aisha Ibrahim a Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara da harsasai 975.

A watan Janairu, jami'an hukumar sun kama Sakina Muhammad da Badariyya Abubakar a kan hanyar Wukari zuwa Jalingo a Jihar Taraba.

Ana zargin an same su da bindigar AK-47 guda daya da harsasai 105 na babbar bindigar mashin (GPMG) da kuma AK-47 guda 14.