| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Nijeriya za ta iya samar da wata hanyar wadatuwar mai a yayin rikicin Gabas ta Tsakiya - Tuggar
Yawan man da Nijeriya ke samarwa ya ƙaru zuwa kusan ganga miliyan 1.7 a kowace rana daga miliyan 1.4 lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki a 2023, bayan ƙalubalen rashin zuba jari, sata da lalata bututun mai da ta daɗe tana fama da su.
Nijeriya za ta iya samar da wata hanyar wadatuwar mai a yayin rikicin Gabas ta Tsakiya - Tuggar
Nijeriya za ta iya samar da wata hanyar wadatuwar mai a yayin rikicin Gabas ta Tsakiya - Tuggar / Reuters
3 awanni baya

Ministan harkokin wajen Nijeriya ya bukaci ƙasashe masu masu samar da mai da iskar gas na yankin Gulf da su dauki ƙasar a matsayin abokiyar hulda, ba abokiyar hamayya ba, don taimakawa da wata hanya ta samar da man fetur a lokacin rikicin.

Rikicin Gabas ta Tsakiya ya bayyana dalilin da ya sa ƙasashe masu arzikin samar da mai da iskar gas daga yankin Gulf su dauki Nijeriya a matsayin abokiyar hulda, ba abokiyar hamayya ba, don ta taimakawa wajen samar da wata hanya ta samar da mai a lokacin rikicin, kamar yadda Ministan Harkokin Waje na Nijeriya Yusuf Tuggar ya shaida wa Reuters.

Wannan jawabin ya zo ne yayin da yaki a Iran ya kawo cikas ga jigilar kayayyakin mai ta mashigin Hormuz, hanya da ake bi da kusan kashi biyar na albarkatun mai da duniya ke amfani, wanda ya tilasta wa masu fitar da kaya dakatar da jigilar kayayyaki tare da haifar da hauhawar farashi.

Rumbun ajiyar mai na Nijeriya da ba a yi amfani da shi ba, zai bai wa ƙasashen Gulf wata dama ta samun danyen mai da iskar gas a daidai lokacin da hanyoyin samar da kayayyaki na duniya ke ƙara zama masu rauni sannan ana sa ran za a ci gaba da samun bukatar iskar gas a tsawon shekaru, in ji Tuggar.

"Ya yi daidai da abin da muka daɗe muna fafutuka akai - cewa ƙasashen da suke kallonmu a matsayin abokan hamayya su hada kai da mu kuma su zuba jari don su iya faɗaɗa kasuwarsu, idan suka yi aiki tare da mu," in ji shi.