Iran ta ce ta kama wani jirgin ruwa ɗauke da lita miliyan 4 ta fetur da aka yi fasa-ƙwauri a Gulf
Iran ta kasance tana neman daƙile fasa-ƙwaurin fetur da ake yi ta kan iyakarta ta ƙsa zuwa ƙasashe maƙabta da kuma ta ruwa zuwa ƙasashen yankin Gulf.
Iran ta karbe wani jirgin ruwan dakon mai na ƙasashen waje a kusa da tsibirin Iran na Qeshm a yankin Gulf, tana mai cewa yana ɗauke da lita miliyan huɗu ta man da aka shigo da shi ba bisa ka'ida ba, in ji kafofin yada labarai na gwamnati a ranar Jumma'a.
Hukumomi ba su bayyana sunan jirgin ko ƙasar da ya fito ba. Sun ce an tsare ma'aikatan jirgin guda 16 na ƙasashen waje ana tuhumarsu da laifuka. Gidan talabijin na gwamnati ya ce an ƙwace tankar a ranar Laraba.
Shafukan labarai na intanet na Iran sun wallafa bidiyo da hotuna na abin da suka ce shi ne jirgin da aka karɓe.
Iran ta ce a makon da ya gabata ta karbe wata tankar mai ta ƙasashen waje da ke ɗauke da lita miliyan shida na dizal da take cewa an shigo da shi ba bisa ka'ida ba a Tekun Oman, ba tare da bayyana sunan jirgin ko ƙasar da ya fito ba.
Iran, wacce ke da ɗaya daga cikin mafi rangwamen farashin mai a duniya saboda manyan tallafi da kuma mummunar faɗuwar darajar kudin ƙasa, na ƙoƙarin dakile yawaitar safarar mai ba bisa ƙaida ba ta ƙasa zuwa ƙasashen makwabta da kuma ta teku zuwa kasashen Gulf.