Wasu wayoyin hannu da aka yi odarsu a shekarar 2010 sun isa Libya bayan shekaru 16

Da mai aiken da wanda zai karɓa suna zaune ne 'yankilomita kaɗan da juna, amma soboda yaƙi sakon bai isa inda ya kamata ba.

By
Daga ƙarshe dai wani ɗan ƙasar Libya ya karɓi wayoyin Nokia da aka yi odar su a shekarar 2010. / TRT World

Wani dilan wayar hannu a Tripoli na ƙasar Libya, ya ƙarɓi wasu wayoyin hannu samfurin Nokia da ya yi odarsu a shekarar 2010, bayan jinkirin tsawon shekaru mai ban mamaki na shekaru 16.

Kayan da aka yi zaton sun ɓace ne, sun haɗa da samfuran wayar Nokia mai tocila kana masu madanna da waɗanda ake sauraro kiɗa da kuma na'urorin "Communicator" na farko da aka fara gani a matsayin fasahar zamani.

Kayayyakin sun makale ne sakamakon yakin basasar Libya a shekarar 2011 da kuma rugujewar hukumar fasa kwauri da sufuri na ƙasar

Da mai aiken da wanda zai karɓa suna zaune ne 'yankilomita kaɗan da juna a Tripoli, amma saboda tsananin yaƙi da rashin kwanciyar hankali aka mance da kunshin sakon a rumbun ajiya na tsawon fiye da shekaru 10.

Rikicin da ya daɗe

Bidiyon mai shago yana buɗe tsofaffin wayoyin da suka shafe shekaru masu yawa a aijiye ya yaɗu a shafukan sada zumunta.

A cikin bidiyon, yana dariya tare da abokansa inda yake raha yana tambaya ko na’urorin ‘‘wayoyi ne ko kuma kayan tarihi ne.’’

Hakan ya nuna irin yadda fasahar wayar hannu ta samu ci gaba tun daga shekarar 2010.

Labarin ya jawo dariya da fashin baki ta intanet, inda masu amfani da dama suke bayyana lamarin da yadda rikici da ya daɗe ke iya haifar da koma baya ga ayyukan kasuwanci da kuma ci gaba a ƙasa.

Wasu kuma sun yi hasashen cewa wayoyin da suka tsufa a yanzu za su iya zama masu daraja a matsayin kayayyakin tarihi.

A lokuta da dama akan danganta yaƙe-yaƙe da yawan mutanen da suka mutu ko wata yarjejeniya da aka cim ma a hukumance. Amma a zahiri, asarar da yake haifar wa a bayyane na da yawa da kuma ban tsoro- kamar dai isar da kaya wanda ya shafe shekaru goma sha shida kafin ya isa inda ake so.