Kotun Ɗaukaka Ƙara a Nijeriya da ke Abuja ta soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya wanda ya umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta cire rajistar Jam’iyyun ADC da Accord Party da kuma wasu jam’iyyu uku.
Kotun ta bayyana cewa hukuncin da ya umarci INEC ta soke rajistar jam’iyyun ba shi da inganci kuma ba shi da wani tasiri a doka.
Tun da farko, Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya umarci INEC ta cire rajistar jam’iyyun bisa yadda suka taka rawar gani a babban zaɓen shekarar 2023.
Sai dai jam’iyyun da abin ya shafa, ciki har da ADC, Action Peoples Party (APP), Action Alliance (AA), Accord Party (AP) da Zenith Labour Party (ZLP), sun ɗaukaka ƙara suna neman a soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya, kuma Kotun Ɗaukaka Ƙara ta amince da buƙatarsu.
Sai dai Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bayyana hukuncin Babbar Kotun Tarayyar a matsayin wanda ba shi da wani inganci a doka, tana mai cewa abin da kotun ta yi ya kai matsayin keta hurumin shari'a, ko kuma abin da Kotun Ƙoli ta taɓa kira rashin biyayya ga tsarin shari'a (judicial insubordination).
Kwamitin alƙalai uku na Kotun Ɗaukaka Ƙarar, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Abba Mohammed, ya yanke hukuncin bai ɗaya cewa tun farko Babbar Kotun Tarayya ba ta da hurumin sauraron ƙarar.
Kotun ta kuma ce Babbar Kotun Tarayyar ta yi kuskure da ta ci gaba da yanke hukunci duk da cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara ta riga ta ba da umarnin dakatar da duk wani ci gaba da shari'ar, ciki har da yanke hukunci.
Haka kuma, Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta ce wanda ya shigar da ƙarar tun farko ba shi da hurumin doka (locus standi) na yin hakan, lamarin da ya sa ta soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya baki ɗaya.

















