AFIRKA
2 minti karatu
Issa Tchiroma Bakary ya yi iƙirarin lashe zaɓen shugaban ƙasar Kamaru
Ɗan takarar jam'iyyar hamayya Issa Tchiroma Bakary ya yi kira ga Paul Biya ya amsa shan kaye ko da yake gwamnati ba ta ce uffan ba game da iƙirarin da ya yi na lashe zaɓen shugaban ƙasar Kamaru.
Issa Tchiroma Bakary ya yi iƙirarin lashe zaɓen shugaban ƙasar Kamaru
Issa Tchiroma Bakary ya yi kira ga Paul Biya ya amsa shan kaye ko da yake gwamnati ba ta ce uffan ba game da iƙirarin da ya yi na samun nasara
14 Oktoba 2025

Ɗan takarar jam'iyyar hamayya a Kamaru Issa Tchiroma Bakary ranar Litinin da tsakar dare ya yi iƙirarin lashe zaɓen shugaban ƙasar wanda aka gudanar ranar Lahadin da ta gabata, sannan ya yi kira ga Paul Biya da ya amsa shan kaye tare da “martaba gaskiyar da ta bayyana ta hanyar masu zaɓe”.

"Nasarar da muka samu a bayyane take. Dole a amshe ta," a cewar Tchiroma a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook daga garinsu na Garoua.

"Mutane sun zaɓi wanda suke so. Kuma dole a mutunta hakan."

Tchiroma Bakaray, mai shekara 76, shi ne tsohon mai magana da yawun gwamnati kuma tsohon minista, wanda ya raba gari da Paul Biya a farkon shekarar nan inda ya ƙaddamar da gagarumin yaƙin neman zaɓe da ya samu karɓuwa daga ɗimbin jama’a da kuma wani ɓangare na ‘yan adawa da ƙungiyoyi masu zaman kansu.


Ko da yake an amince a riƙa bayyana sakamakon zaɓe, sai dai kotun tsarin mulkin Kamaru ce kaɗai take da alhakin sanar da sakamakon ƙarshe, kuma ba a yarda “kowa ya yi gaban kansa ba”.

A zaɓen shugaban ƙasa na 2018, ɗan takarar jam’iyyar hamayya na wancan lokaci Maurice Kamto ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen kwana guda bayan kammala kaɗa ƙuri’a.

Daga bisani an kama shi sannan aka yi amfani da barkonon-tsohuwa da ruwan zafi wajen tarwatsa magoya bayansa da suka yi zanga-zanga.

Paul Biya, mai shekara 92, wanda shi ne shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya, yana neman yin ta-zarce a karo na takwas bayan ya shafe shekaru 43 a kan mulki.

Tchiroma ya yaba wa masu kaɗa ƙuri’a kan bijire wa barazanar da gwamnati ta yi musu inda suka kafa suka tsare har sai da aka sanar da sakamakon zaɓuka a akwatunan zaɓensu.

"Kazalika ina miƙa godiyata ga ‘yan takara waɗanda suka suka aiko mini da saƙonnin taya murna kana suka amince da ƙarfin ikon mutane," in ji Tchiroma Bakary.

Gwamnatin Kamaru ba ta ce uffan ba game da iƙirarin da Tchiroma Bakary ya yi na lashe zaɓen shugaban ƙasar, sai dai Ministan Gudanarwa Paul Atanga Nji ya yi gargaɗi a ƙarshen mako cewa duk ɗan takarar da ya yi gaban kansa wajen ayyana kansa a matsayin shugaban ƙasa, zai iya fuskantar hukuncin “cin amanar ƙasa”.

Ya ƙara da cewa kotun tsarin mulkin ƙasar ce kawai take da ikon sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar.

Rumbun Labarai
Sojojin Sudan sun harbo jirgi maras matuƙi na RSF a Kordofan ta Arewa
Dakarun Nijar sun cafke muggan makamai da aka yi safararsu daga Libya, sun kama masu safarar ƙwayoyi
RSF ta Sudan ta kai hare-hare a Jihar Khartoum da birnin Atbara bayan amincewa da tsagaita wuta
Paul Biya na Kamaru: Shugaban da ya fi tsufa a duniya ya sha rantsuwar kama aiki karo na takwas
Hatsarin mota ya yi ajalin fiye da mutum 1,000 a Nijar a shekarar 2023, fiye da 12,000 sun jikkata
Sabbin hotunan tauraron dan'adam sun gano alamun 'kaburburan bai-daya a El-Fasher a Sudan
MDD ta yi gargaɗin cewa yaƙin Sudan na gurgunta tattalin arzikin Sudan ta Kudu
Trump ya ce bai kamata Afirka ta Kudu ta kasance cikin G20 ba, ba zai je taronta a Johannesburg ba
'Yan Sudan sun ba da mummunan labarin yi wa mata fyade yayin da suke tserewa daga Al Fasher
An kashe mutane 40 a harin da aka kai wa taron jana'iza a yankin Kordofan na Sudan: MDD
Yadda biranen Afirka mafiya tsafta suke bayyana sauyin da ake samu a nahiyar
Sojojin Ruwa na Ghana sun kama ‘yan Nijeriya 10 da suka ɓuya a jirgin ruwan Panama a Tema
Harin jirgin sama maras matuƙi na RSF ya kashe mutane da dama a lardin Kordofan na Arewa a Sudan
Fiye da mutum 1,500 sun rasa matsugunansu a Sudan sakamakon taɓarɓarewar tsaro: MDD
Dakarun RSF sun kashe mata 300, sun yi wa 25 fyaɗe cikin awa 48 a Al Fasher – Minista
Amurka ta buƙaci a tattauna domin kawo ƙarshen yaƙin Sudan, ba amfani da ƙarfin soja ba
Ana fargabar dubban mutane na cikin 'mummunan hatsari' a birnin Al Fasher na Sudan da RSF ta ƙwace
Shugabar Tanzania Samia Hassan ta lashe zaɓen ƙasar da kashi 97.66 cikin 100
Tchiroma Bakary: Sojojin Kamaru sun yi wa jagoran 'yan adawar kasar rakiya zuwa wuri mai 'aminci'
Kudirin 1325 ya cika shekara 25: Me ya sa dole Afirka ta jagoranci samar da zaman lafiya a duniya