Shugaban Amurka Donald Trump ya fi ba da fifiko ga tattaunawar diflomasiyya da Tehran duk da mastin da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu yake yi na ƙaddamar da sabbin hare-haren soji nan-take bayan zaɓukan tsakiyar wa’adi na Amurka na ranar Talata, in ji wani rahoton kafofin watsa labaran Amurka.
A wata tattaunawa ta waya ta ranar Asabar, shugaban Isra’ila ya matsa wa Washington ta kai sabbin hare-haren soji kan Iran da zarar an kammala zaɓen, amma Trump ya fi mayar da hankali kan ba da dama ga tattaunawar diflomasiyyar da ake yi, in ji majiyoyi na Amurka da Isra’ila da ke da masaniya game da musayar ra’ayin, kamar yaɗa kafar Axios ta ruwaito ranar Lahadi.
Netanyahu ya “damu” game da hanyar da Trump ke bi, in ji majiyoyin.
Jami’in Isra’ilan ya kuma bayyana tattaunawar a matsayin mai "tsauri," yayin da majiyar Amurka ta bayyana ta a matsayin "ta ƙeƙe-da-ƙeƙe."
Trump ya shaida wa manema labarai cewa ya tattauna da Netanyahu game da Iran ranar Asabar, yana mai cewa sun yi wata tattaunawa "mai matuƙa kyawu”
A baya dai, shugaban Amurka ya ce tattaunawa da Tehran na tafiya yadda ya kamata, yana mai ƙarawa da cewa ba ya "cikin gaggawa" don fara kai hare-hare, duk da cewa a baya ya nuna alamar kai ƙarin hare-hare bayan ranar 3 ga watan Nuwamba.
An zafafa ƙoƙarin diflomasiyya
Matsin da Netanyahu yake yi na sabunta kai hare-hare na zuwa ne a yayin da ake ƙoƙarin farfaɗo da tattaunawa a hukumance, bayan saƙon da mataimakin shugaban ƙasar Amurka JD Vance ya tura wa Mohsen Rezaei, sakataren majalisar ƙoli ta tsaron Iran, kan yiwuwar fara sabuwar tattaunawa a hukumance.
A wani ɓangaren kuma, masu shiga tsakani na Qatar suna tattaunawa da wakilan Iran domin komawa kan teburin tattaunawa kai-tsaye.
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce suna jiran amsoshi daga Amurka, yana mai cewa babu wata tsayayyiyar yarjejeniya kawo yanzu.
Fadar White House da ofishin Firaministan Isra’ila sun ƙi yin toskaci kan rahoton, in ji Axios.













