Kotun Bangladesh ta yanke wa Sheikh Hasina hukuncin kisa
“Duk wasu shika-shikan aikata laifuka kan bil’adama sun cika,” in ji alkalin kotun, Golam Mortuza Mozumder, yayin da yake karanta hukuncin ga kotun da ta cika maƙil a Dhaka.
Wata kotu a Bangladesh a ranar Litinin ta yanke wa tsohuwar Firaminista Sheikh Hasina hukuncin kisa kan laifukan cin zarafin bil’adama, inda aka yi ta murna a cikin kotun da a yayin da alƙali ke karanto hukuncin.
An bayyana cewa Hasina, mai shekaru 78, ta ƙi bin umarnin kotu da ke buƙatar ta dawo daga Indiya domin ta halarci shari’arta kan zargin cewa ta umarci amfani da ƙarfi wurin daƙile zanga-zangar ɗalibai wadda ta kai ga kifar da gwamnatin ta.
Wannan hukunci da jama’a suka dade suna jira, wanda aka watsa kai tsaye a talabijin na ƙasa, ya zo ne kafin zaɓen farko tun bayan kifar da ita a watan Agustan 2024.
“Duk wasu shika-shikan aikata laifuka kan bil’adama sun cika,” in ji alkalin kotun, Golam Mortuza Mozumder, yayin da yake karanta hukuncin ga kotun da ta cika makil a Dhaka.
An bayyana cewa an same ta “da laifi a tuhuma uku,” ciki har da hura wutar tashin hankali, bayar da umarnin kashe mutane, da kuma rashin ɗaukar mataki don hana aikata munanan abubuwan da aka aikata, in ji Mozumder
“Mun yanke shawarar yanke mata hukunci guda ɗaya — wato hukuncin kisa.”