Shugaban kamfanin Kayan Sufurin Sararin Samaniya na Turkiyya (TAI), Mehmet Demiroglu, ya bayyana cewa kasar Sifaniya na shirin sayen karin jiragen bayar da horo samfurin Hurjet guda 15 daga kasar Turkiyya, bayan da aka riga aka rattaba hannu kan yarjejeniyar sayen jirage 30.
Da yake jawabi a wani taron da aka gudanar a lardin Kastamonu dake arewacin Turkiyya, Demiroglu ya ce ana sa ran fara kai jiragen zuwa kasar Sifaniya a shekarar 2028.
"Tun kafin mu fara kai jiragen ga Rundunar Sojin Samanmu, kasar Sifaniya ta nuna sha'awarta tare da cewa 'Muna son su, muna son sayen guda 30,' kuma suka saye su. Mun rattaba hannu kan yarjejeniyar," in ji shi. "Muna aiki tukuru domin ganin an kai jiragen a shekarar 2028. Yanzu kuma suna shirin sayen karin wasu guda 15."
Har ila yau, Demiroglu ya yi karin haske kan karfin samar da kayayyaki na kamfanin TAI, inda ya bayyana cewa cibiyar kamfanin tana tattare ayyukan kera jiragen yaki samfurin Kaan, jiragen Hurjet da Hurkus, jiragen sama masu saukar ungulu, jiragen sama marasa matuki, tauraron dan adam, da kuma sassan jiragen sama.
Kamfanin na gudanar da gwaji da samar da kayayyaki a fannoni shida, in ji shi, yana mai bayyana ta a matsayin alfaharin ƙasa.
Demiroglu ya ce an fara mika jiragen saman Hurkus kuma za su ci gaba a cikin shekaru masu zuwa. Ya gano Azerbaijan a matsayin wurin fitar da kayayyaki kuma ya ce kamfanin yana da niyyar tabbatar da ƙarin sayar da jiragen a ƙasashen waje.
Demiroglu ya ce masana'antar tsaro ta Turkiyya ta ƙarfafa matsayin ƙasar a duniya kuma ta haifar da sha'awar duniya ga fasaharta.
"A cikin shekarun 2020, musamman tare da nasarorin da aka samu a masana'antar tsaro, babban yabo ga Turkiyya ya bayyana a duk faɗin duniya," in ji shi. "Suna yabawa kayayyakinmu, abin da muke yi da nasarorin da muka samu."
‘Muna samar da su ne, ba lallai mu yi mfani da su ba’
Ya bayyana matakin hana kai hari a matsayin babbar manufar shirye-shiryen tsaron Turkiyya, ciki har da jirgin saman yaki na Kaan.
"Ba muna aiki ne don mu yi yaki ba. Muna bukatar yin aiki ne domin kauce wa yaki," in ji Demiroglu, yayin da yake jaddada bukatar shirya rundunar sojin Turkiyya da kuma kasar baki daya domin tunkarar barazanar tsaro.
"Ba ma son yin amfani da Kaan," ya kara da cewa. "Muna kera shi ne domin kada mu taba bukatar yin amfani da shi."
Yayin da yake jawabi ga dalibai a wajen taron, Demiroglu ya karfafa gwiwar matasa su bunkasa kwarewarsu tare da koyon fasahohin da za su horar da su domin makomar nan gaba.
Ya yi nuni da cewa fadada bikin TEKNOFEST, wanda ke mayar da hankali kan fasahar sararin samaniya da sauran fasahohi, na taimakawa wajen karfafa burin mutane a fannin fasaha.



























