Rundunar sojin Nijeriya ta kuɓutar da masu yi wa ƙasa hidima 47 daga 'yan Boko Haram a Borno

Sojojin sun yi saurin kuɓutar da su daga yiwuwar garkuwar ‘yan Boko Haram/ISWAP, waɗanda ke kai hare-hare yankin,’’ in ji sanarwar.

By
Rundunar sojin Nijeriya ta kubutar da masu yi wa kasa hidima 47 / Reuters

Rundunar Haɗin Kai ta sojojin Nijeriya (JTF) ta Arewa maso Gabashin ƙasar ta kuɓutar da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) su 47 daga yunƙurin garkuwar 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP a kan hanyar Buratai zuwa Kamuya a Jihar Borno.

Mai magana da yawun rundunar, Sani Uba ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a da ya fitar ranar Alhamis.

"An ceto 'yan bautar ƙasa, maza 36 da mata 38, da misalin karfe 9:05 na dare a ranar Talata bayan da motocinsu suka lalace kusa da wani wuri da aka san ana garkuwa da mutane," in ji Uba.

A cewarsa, an tura wata tawagar jami’an sintiri ta sojoji cikin gaggawa zuwa wurin bayan da wata na'urar talabijin ta CCTV da sojoji ke sa ido a kai ta gano motsin motocin bas uku a wurin da ake zargi.

"Da isowarsu, sojoji sun gano 'yan NYSC 74 da suka makale bayan da motocinsu suka samu matsalar inji.”

Sojojin sun yi saurin kubutar da su daga yiwuwar garkuwar ‘yan Boko Haram/ISWAP waɗanda ke kai hare-hare yankin,’’ in ji sanarwar.

Kazalika, sanarwar ta ƙara da cewa, a yanzu haka 'yan NYSC ɗin da aka ceto suna sansanin sojoji na Buratai kafin a ci gaba da shirye-shiryen tafiya kai su wuri mai aminci.