| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Farashin man fetur a Nijeriya ya tashi da kashi 643% a cikin shekaru uku — Rahoto
Tashin farashin na baya bayan nan ya faru ne daga kimanin N800 da ake sayar da litar man cikin ‘yan watannin da suka gabata zuwa N1,300 sakamakon tashin hankalin da ake yi a Gabas Ta Tsakiya, lamarin da ya janyo tsaiko a harkar samar da mai a duniya.
Farashin man fetur a Nijeriya ya tashi da kashi 643% a cikin shekaru uku — Rahoto
TSOHON HOTO: Yayin da farashin mai ya haura sama, layuka a gidajen mai sun yi sauƙi / Reuters

A Nijeriya farashin man fetur ya tashi daga N175 zuwa N1,300 tsakanin watan Mayun shekarar 2023 zuwa watan Mayun 2026, wani matakin da ya kai kashi 643 cikin 100 a cikin shekaru uku, kamar yadda jaridar The PUNCH ta Nijeriya ta ruwaito.

Jaridar ta ce bincikenta ya nuna cewa hawhawar farashin man fetur ɗin ya faru ne sakamakon cire tallafin man fetur da Shugaba Bola Tinubu ya yi jim kaɗan bayan an rantsar da shi ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2023.

Kazalika matakin da gwamnatinsa ta ɗauka na dakatar da tsarin ƙayyade farashin dala ya dagula lamarin, inda ya sa farashin man da a wancan lokacin ake shigar da shi ƙasar ne ya tashi fiye da abin da ‘yan Nijeriya da dama za su iya saya.

Bayan shekaru uku, farashin litar man fetur a gidajen mai ya yi tashin gauron zabi, inda ake sayar da shi tsakanin N1,300 zuwa N1,400, dangane da wurin da gidan mai yake.

Tashin farashin na baya bayan nan ya faru ne daga kimanin N800 da ake sayar da litar man cikin ‘yan watannin da suka gabata zuwa N1,300 sakamakon tashin hankalin da ake yi a Gabas ta Tsakiya, lamarin da ya haifar da tsaiko a harkar samar da mai a duniya sakamakon rufe Mashigar Hormuz.

Idan za a iya tunawa a lokacin rantsuwar kama aikin Shugaba Tinubu ne ya sanar da cewa “tallafin mai ya tafi.”

Wannan ya janyo tashin farashin mai nan take daga N175 ko N200 zuwa sama da N500 kan kowace lita. Kamfanin mai na Nijeriya NNPC, wanda shi kaɗai ne yake shigar da man fetur a lokacin, shi ne ya jagoranci ƙarin farashin man ta hanyar ɗaga farashinsa a gidajen mansa.

Rumbun Labarai
Tsayar da Obi ɗan takarar NDC ya sake share fagen fafatawar manyan 'yan takara uku a Nijeriya
NAHCON ta ba da umarnin bincike kan wani abinci da mahajjata suka ƙi ci kan 'rashin inganci'
Masu tayar da ƙayar baya 30,000 na rura wutar rashin tsaro a Nijeriya - Rahoton Amurka
'Yanbindiga sun yi garkuwa da mutum 10 tare da kona gidan wani sarki a jihar Kwara a Nijeriya
Sojojin Nijeriya sun kashe ‘yanta’adda 12 da ƙwato makamai a Borno
Wa zai fafata da Tinubu? Jam'iyyun siyasar Nijeriya na zaɓen fitar da 'yan takarar shugabancin ƙasar
Kotu ta soke jadawalin INEC game zabukan fitar da gwani da tsayar da 'yantakara na 2027
Tinubu ba shi da shirin sauya sunan Nijeriya ko soke shari'ar Musulunci a arewa – Fadar gwamnati
Hukumar Alhazan Nijeriya ta kammala jigilar maniyyatan ƙasar zuwa Saudiyya
Fitaccen Fasto a Nijeriya ya ba magoya bayan Arsenal haƙuri kan 'saƙon wahayin ƙarya' da ya isar
Wasu sun nemi na mutu saboda tallafin mai da canjin dala— Tinubu
NDLEA ta tarwatsa ƙungiyar masu hada miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya da Mexico ta kama mutum 10
Sojojin Nijeriya 'bakwai ne' suka mutu a wani harin kwanton ɓauna na'yanta'adda a Jihar Sokoto
An kashe shugabannin Daesh 175 a arewa maso gabashin Nijeriya a farmakin haɗaka da Amurka
An sace yara da manya 46 a hare-haren makarantu a kudancin Nijeriya
Rundunar Sojin Amurka da ke aiki a Afirka ta ƙara kai sabbin hare-hare kan 'yanta'adda a Nijeriya
Babbar Kotun Tarayya a Abuja Nijeriya ta ba da belin Nasir El-Rufai kan naira miliyan 100
Nasarori da jayayya da mamaki sun karaɗe zaɓukan fid da gwani na Majalisar Wakilan APC a Nijeriya
Nijeriya ta tsananta sa ido bayan WHO ta ayyana dokar ta-baci kan Ebola da ta kashe mutum 88 a Congo
Rundunar 'yansandan Nijeriya ta tabbatar da kashe jami'anta 17 a harin ta'addanci a Jihar Yobe