Tawagar Argentina ta yunƙuro daga baya ta doke Masar da ci 3-2 a wasan zagaye na ƙasashe 16 da suka fafata ranar Talata, bayan Masar ta zura mata ƙwallo biyu a raga har zuwa kusan minti na 80 da fara wasan.
Yasser Ibrahim ne ya zura ƙwallo a ragar Argentina da kai a minti 15 da fara wasa.
Daga baya Argentina ta yi ƙoƙarin farke wa, inda ta samu bugun fenareti, amma golan Masar ya tare fenaretin da Lionel Messi ya buga minti 20 da fara wasa.
Sai miniti 58 da fara wasa inda Mostafa Ziko ya zura ƙwallo a ragar Argentina, amma an soke ƙwallon saboda ƙetar da aka yi wa ɗan Argentina kafin a tafi zura ƙwallon a raga.
Mostafa Ziko bai gajiya ba domin minti 67 da fara wasa ya sake zura ƙwallo a ragar Argentina, lamarin da ya mayar da ƙallon 2-0.
Amma Cristian Rimero ya farke wa Argentina ƙwallo ɗaya a minti 79 da fara wasa inda wasan ya koma 2-1.
Sai a minti 83 kuma Lionel Messi ya farke wa Argetina ƙwallo ta biyu inda wasan ya koma 2-2.
Sannan a minti na 93 Enzo Fernandez ya zura wa Argentina ƙwallo na uku a raga lamarun da ya mayar da wasan 3-2.
A yanzu dai Argetina ce za ta tafi matakin kwata final.













