Mali ta musanta rahoton sakin ’yanta’adda 200 domin samun man fetur

Tun daga shekarar 2012, ƙasar Mali take fuskantar barazanar tsaro mai tsanani daga ƙungiyoyi masu alaƙa da Al-Qaeda, gami da wasu gungun masu aikata laifuka na cikin gida.

By
Rundunar sojin Mali ya musanta cewa Bamako ta yi shawara kan sakin wadanda ake zargi da ta'addanci domin a samu damar fitar da mai ba / User Upload

Rundunar sojin ƙasar Mali ta musanta rahoton da ke cewa ta saki kusan mutane 200 da ake zargin ’yanta’adda ne a tsakiyar watan Maris, da nufin dakatar da hare-haren da ake kai wa ayarin motocin dakon mai.

Souleymane Dembele, daraktan yada labarai da hulda da jama’a na rundunar sojin ƙasar, ya shaida wa manema labarai a ranar Litinin cewa “wadannan kalaman, waɗanda wasu kafafen yaɗa labarai suka ruwaito, an yi su ne da nufin ɓata sunan Mali da kuma sanya shakku a zukatan jama’a don rusa amincin da ke tsakanin al’umma da hukumominsu, musamman tsakanin al’ummar Mali da dakarun kasar.”

Ya ƙara da cewa, “Wannan tsantsar makirci ne, ba shi da tushe ballantana makama, sannan babu wata majiya sahihiya da ta tabbatar da hakan.”

Tun daga watan Satumban 2025, wata ƙungiyar ’yanta’adda mai alaƙa da Al-Qaeda take kai wa ayarin motocin dakon mai hari, lamarin da ya taba sa rayuwa ta tsaya cik a birnin Bamako lokacin da rikicin ya yi tsanani a watan Oktoba.

Karancin Man Dizal

Mazauna birnin Bamako sun kuma fuskanci ƙarancin man dizel a farkon watan Maris, inda aka ba wa ɓangaren makamashi fifiko wajen amfani da man da ake da shi.

Tun daga shekarar 2012, ƙasar Mali take fuskantar barazanar tsaro mai tsanani daga ƙungiyoyi masu alaƙa da Al-Qaeda, gami da wasu gungun masu aikata laifuka na cikin gida