Wani kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya tabbatar da cewa babban jami’in diflomasiyya Abbas Araghchi ya isa babban birnin Pakistan, amma ba za a yi wata tattaunawa kai-tsaye da Amurka ba.
Esmaeil Baqaei ya fada a ranar Asabar cewa Araghchi zai gana da manyan jami’an Pakistan.
Ministan Harkokin Wajen Pakistan Ishaq Dar da Babban Hafsan Sojin kasar, Field Marshal Asim Munir, da sauran manyan jami’ai ne suka tarbi Araghchi lokacin da ya isa.
Baqaei ya rubuta a shafin X cewa tattaunawar za ta gudana ne “tare da kokarin shiga tsakani da kuma kyakkyawar niyya” don taimakawa wajen kawo karshen “yaƙin zalunci da Amurka ta ƙaddamar” da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.
“Ba a tsara wani taro da zai gudana tsakanin Iran da Amurka ba. Za a isar da bayanan Iran ga ƙasar Pakistan,” in ji shi.
Wannan tattaunawa na zuwa ne yayin da Pakistan ke ci gaba da kokarin shiga tsakani da nufin rage taƙaddama tsakanin Iran da Amurka.
Tun da farko, Kakakin Fadar White House, Karoline Leavitt, ta ce manzon musamman na Amurka, Steve Witkoff, da surukin Shugaba Donald Trump, Jared Kushner, za su tafi Pakistan a ranar Asabar don tattaunawa da wakilan Iran.
“Zan iya tabbatar da cewa manzon musamman Steve Witkoff da Jared Kushner za su tafi Pakistan gobe da safe don yin tattaunawa kai-tsaye, karkashin jagorancin Pakistan wadda ta nuna bajinta wajen shiga tsakani a dukkan wannan tsari, tare da wakilai daga tawagar Iran,” Leavitt ta shaida wa kafar labarai ta Fox News.
Ta ƙara da cewa Mataimakin Shugaban Kasa, JD Vance, zai zauna a Amurka, kodayake “yana nan da masaniya sosai a cikin dukkan wannan tsari.”
Leavitt ta shaida wa manema labarai cewa shugaban ya yanke shawarar tura Witkoff da Kushner ne “domin su saurari abin da Iraniyawa ke da shi.”
“Tabbas mun ga wasu ci-gaba daga ɓangaren Iran a cikin ’yan kwanakin nan,” in ji Leavitt. Sai dai ba ta bayar da cikakken bayani kan abin da jami’an Amurka suka ji ba.
Pakistan na ƙara ƙaimi wajen ganin an sake ƙaddamar da zagaye na biyu na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka.
Majiyoyi sun ce tattaunawar da za a yi da Iran na iya share fage ga sabuwar tattaunawa biyo bayan zagayen farko na tattaunawa kai-tsaye da aka yi a Islamabad ranar 11-12 ga Afrilu.
Waccan tattaunawa ta zo ne bayan Pakistan ta samar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako biyu a ranar 8 ga Afrilu, wanda daga baya Trump ya tsawaita ba tare da bayyana takamaiman lokacin da zai ƙare ba.
Waɗannan ci gaba na zuwa ne a yayin da ake ciki da taƙaddama tun bayan ɓarkewar yaƙi a ranar 28 ga Fabrairu, inda aka mayar da hankali kan cim ma yarjejeniya mai faɗi don kawo ƙarshen yaƙin.
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Iran ta ce ba kai-tsaye za a yi tattaunawa a Pakistan don kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Isra’ila ba
Yayin da babban jami’in diflomasiyyar Iran, Abbas Araghchi, ya isa Islamabad, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmaeil Baqaei, ya ce za a isar da korafe-korafen Iran ga Pakistan, a daidai lokacin da Amurka ta tura Kushner da Witkoff Pakistan.

Rumbun Labarai
















