Cikin Hotuna: An yi bikin auren gomman Falasɗinawa a Gaza a lokaci guda

Aure 54 ne aka ɗaura a wani biki na mutane da yawa da aka yi cikin ɓaraguzan Khan Younis, wanda Isra'ila ta haddasa.

By
Falasɗinawa sun halarci auren mutum 54 a Khan Younis / AP

Eman Hassan Lawwa ta saka kaya irin na al’adar Falasɗinawa kuma Hikmat Lawwa ya saka a kwata da wando inda suka taho hannu-da-hannu cikin ɓaraguzan gine-gine a kudancin Gaza a cikin wani jerin ma’aurata da suka saka kaya irin nasu.

Falasɗinawan masu shekara 27 da haihuwa suna cikin ma’aurata 54 da aka ɗaura wa aure ranar Talata a wani auren da aka ɗaura wa mutane da yawa a cikin wurin da aka yi wa ƙawanya, wani lamarin da ya nuna fata da ba a saba gani ba bayan shekara biyu na kisan ƙare dangi.

"Duk da abin da ya faru, za mu fara sabuwar rayuwa," in ji Lawwa . "Idan Allah ya yarda , wannan zai kasance ƙarshen yaƙin."

Ɗaurin aure wata muhimmiyar al’adar Falasɗinawa ce wadda ta zama abin da ba kasafai ake gani a Gaza ba a lokacin kashe-kashen Isra’ila.

Al’adar ta fara farfadowa bayan yarjejeniyar tsagaita wuta mai rauni da aka yi, duk da cewa ɗaurin auren ya sha bamban da irin biki mai yawa da ake yi a da can a cikin garin.

Yayin da gungun mutane suke ihu kuma suke kaɗa tutar Falasɗinu a birnin kudanci na Khan Younis, rikicin da ake yi a faɗin gaza ya rage armashin bukunuwan.

Yawancin mazauna miliyan 2, ciki har da Eman da Hikmet, sun rasa gidajensu sakamakon kashe-kashen Isra’ila, an shafe wurare a cikin boirnin, kuma ƙrancin kayan agaji da kuma ɓarkewa kisan ƙra dangi na ci gaba da addabar rayuwar yau da kullum na mutanen .

"Muna son mu yi murna kamar sauran duniya . A da ina mafarkin in samu gida da aiki da lkasancewa kaman kowa ," a cewar Hikmet. "A yau , mafarki na shi ne na sami tentin da zan zauna ciki ."

"Rayuwa ta fara komawa, amma ba yadda muka so ba ," kamar yadda ya ƙra bayyana wa .

Al Fares Al Shahim ce ta ɗauki nauyin bikin. Baya ga yin bikin, ƙungiyar ta bai wa ma’auratan kuɗaɗe kaɗan domin su fara rayuwarsu tare.

Ga Falasɗinawa , ɗaurin aure abu ne da ke da bukukuwa da yawa, da ake shafe yini ɗaya ana yi, wanda ake gani a matsayin zaɓi na zamantakewa da tattalin arziƙi da nuna makomar iyalai.

Sun haɗa da rawa mai cike da murna da kuma jerin gwano cikin tituna inda iyalai da yawa masu sanye da atamfa irin na ma’aurata da ‘yan’uwansu da kuma tarin ƙananan farantin abinci.

Ka wasu daga cikin hotunan auren: