Nijeriya ta naɗa sabon kwamandan da zai jagoranci ayyukan soji na yaƙi da ƙungiyar ta’addanci ta Boko Haram da ɓangaren ISWAP da ya ɓalle a jikinta a arewa maso gabashin ƙasar, in ji kakakin rundunar soji a ranar Laraba.
An nada sabon kwamandan ne gabanin zaɓen shugaban ƙasa da aka shirya gudanarwa a watan Janairu, yayin da matsalar tsaro ke ci gaba da zama babban abin damuwa sakamakon shekaru na tashin hankali, ayyukan ’yanbindiga da sace mutane a wasu sassan ƙasar.
Manjo Janar Ibikunle Ademola Ajose, wanda a baya ya yi aiki a hedikwatar rundunar soji da ke Abuja, zai maye gurbin Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, kwamanda na 15 na Operation Hadin Kai, wanda ya karɓi ragamar aikin a watan Afrilun 2025.
A cewar bayanan da Armed Conflict Location & Event Data Project (ACLED) ta tattara, ayyukan ta’addancin Boko Haram da ɓangaren ISWAP da ya balle daga gare ta sun yi sanadin mutuwar fiye da mutane 40,000 tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu tun shekarar 2009.
Sauye-sauyen shugabancin soji
Matsalar tsaro ta kawo cikas ga gudanar da zaɓe a wasu sassan arewa maso gabashin Nijeriya a zaɓen shugaban ƙasa da ya gabata, kuma har yanzu tana ci gaba da zama ƙalubale gabanin zaɓukan shekara mai zuwa.
Rundunar sojin ba ta danganta sauyin kwamandojin da wani sabon hari da aka kai a arewa maso gabashin ƙasar ba.
Kakakin rundunar sojin, Appolonia Anele, ta ce sauyin wani ɓangare ne na babban garambawul da ya shafi wasu janar-janar 14.
Ta ce an gudanar da garambawul ɗin ne domin inganta tasirin ayyukan soji, ƙarfafa shugabanci da kuma daidaita tsarin kwamandoji da sauye-sauyen ƙalubalen tsaron da Nijeriya ke fuskanta.



















