Yadda 'yan Nijeriya suka fusata kan matakin Amurka na saka wa Kwankwaso takunkumi
Wasu ’yan majalisar dokokin Amurka biyar ne suka sanya sunan tsohon gwamnan Jihar Kanon a cikin sunayen mutanen da ke take hakkin addinin a wani kudirin doka da suka gabatar a gaban zauren majalisar dokokin Amurka a ranar Talata.
’Yan Nijeriya suna ci gaba da yi wa kasar Amurka rubdugu bayan da wasu ’yan majalisa a kasar suka ayyana sunan jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a cikin jerin mutanen da ke take hakkin Kiristoci a Nijeriya.
Wasu ’yan majalisar dokokin Amurka biyar ne suka sanya sunan tsohon gwamnan Jihar Kanon a cikin sunayen mutanen da ke take hakkin addinin a wani kudirin doka da suka gabatar a gaban zauren majalisar dokokin Amurka a ranar Talata.
Idan kudirin ya zama doka, hakan yana nufin ma’aikatar harkokin wajen Amurka da ma’aikatar kudin Amurka za su sanya haramcin shiga kasar da kuma kwace kadarorin Kwankwaso a Amurka idan yana da su, sannan kuma kudirin ya buƙaci a ƙwace kadarorin kungiyoyi kamar na Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN), saboda zargin hannu da suke da shi a kisan mabiya addinin Kirista a Nijeriya.
Jam’iyyar NNPP wacce a karkashinta Sanata Kwankwaso ya yi takarar shugabancin Nijeriya a shekarar 2023, ta yi watsi da zargin da ’yan majalisar dokokin suke yi wa fitaccen dan siyasan, inda Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar na Kasa Ladipo Johnson ya ce abin takaici ne sanya sunan Kwankwaso a abin da sam ba shi da masaniya a kansa.
Shi ma mai magana da yawun Kungiyar Kwankwasiyya Movement Dokta Habibu Sale Mohammed ya ce zarge-zargen da ’yan majalisar wakilan Amurkan suka gabatar a kan Kwankwaso ba su da tushe kuma ba gaskiya ba ne, idan aka yi la’akari da yadda tsohon gwamnan ya sadaukar da rayuwarsa wajen kawo wa al’umma ci gaba.
A wata sanarwa da Dokta Habibu ya fitar ta ce tsawon shekaru 30 da suka wuce Sanata Kwankwaso ya rike manyan mukamai a Nijeriya kamar Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai da Gwamnan Kano har wa’adi biyu da Ministan Tsaro da kuma Dan Majalisar Dattawa. Sanarwar ta ci gaba da cewa duk tsawon wannan lokaci ba a taba samunsa da laifin take hakkin addinin ba, ko matsanancin tsatsauran ra’ayin adddini ko kuma laifin take hakkin wani ba.
Sannan sanarwar ta bayar da misalin cewa lokacin da ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2023 ya zabo Bishop Isaac Idahosa, wanda limamin Kirista ne a matsayin mataimakinsa saboda shi mutum ne mai son tafiya da kowa da kowa, ba tare da la’akari da addinin da mutum yake bi ba, in ji sanarwar.
Kazalika sanarwar ta yi watsi da batun kaddamar da shari’ar Musulunci da Kwankwaso ya yi a matsayin hujjar sanya shi a cikin jerin masu take hakkin Kiristoci da ’yan masalisar Amurka suka dogara da ita. Dokta Habibu ya ce ba Jihar Kano ce kadai ta kaddamar wannan tsari ba, abu ne da aka yi a wasu jihohin arewacin kasar da dama, kuma tsari ne da bai saba wa kundin tsarin mulkin Nijeriya ko tsarin shari’ar kasar ba.
Kungiyar Kwankwasiyya Movement ta ce bayyana sunan Kwankwaso a matsayin mai taimakawa wajen take hakkin Kiristoci saboda batun shari’ar Musulunci da ya kaddamar a jiharsa lokacin da yake gwamna rashin adalci ne. Daga nan sanarwar ta bukaci majalisar wakilan Amurka da ta cire sunan jagoran NNPP ba tare da bata lokaci ba.
Shi ma fitaccen lauyan nan mazaunin Birtaniya Dokta Audu Bulama Bukarti ya bayyana Kwankwaso a matsayin dan siyasa mai sassaucin ra’ayi sosai kuma daya daga cikin ’yan siyasa kalilan masu kishin Nijeriya. Masanin shari’ar ya ce bayyana sunan shi a matsayin wanda za a sanya wa takunkumi, hakan ya wuce rashin adalci, daukar wannan matakin kuskure ne karara. A wani sako da ya wallafa a shafin X, Dokta Bukarti ya yi kira ga ’yan majalisar dokokin Amurka da su cire sunansa ba tare da wani bata lokaci ba.
Fitaccen lauyan ya ce wannan abin da ya faru ya kara fito da rauni ta fuskar sahihancin bayanan da Amurka ta dogara da su wajen kaiwa ga matsayar cewa “ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi” a Nijeriya.
Shi ma fitaccen dan jarida kuma mai fashin baki kan harkokin siyasa Jaafar Jaafar ya ce laifi daya da Kwankwaso ya yi shi ne Allah-wadai da barazanar da Shugaban Amurka ya yi na kai hari Nijeriya dangane da zargin kisan mabiya addinin Kirista da ya ce ana yi a kasar a bara. Kwankwaso yana cikin manyan ’yan siyasar kasar da suka bayyana adawarsu a fili ga matsayar da Amurka ta ce za ta dauka kan Nijeriya. Jaafar ya ce Kwankwaso ba shi da tsattsauran ra’ayin addini, kamar yadda ya wallafa a shafin X.
Masanin siyasar ya ce ’yan majalisar Amurka ba su yi wa Kwankwaso adalci ba, idan uka dogara da batun Shari’ar Musulunci suka ayyana shi a matsayin mai take hakkin mabiya addinin Kirista.