Yara mata ne suka fi cutuwa daga yaƙin Sudan da aka manta da shi
Shekaru uku kenan, yakin Sudan ya janyo mutuwar dubban mutane tare da tsugunar da miliyoyi. Baya ga asarar rayuka, akwai wani rikici da ke afkuwa: cin zarafin mata, barin yara mata na shan wahala, sau da yawa a sirrance, neman tsira ya maye yarinta
Lokacin da mayakan RSF suka kai hari kan al Fasher a watan Oktoban 2025, inda suka yi ta kashe-kashe, Abeer da 'yar’uwarta suka hau mota cike da jama'a tare da sauran mutanen kauyen suka gudu - suna rike duk wata dama ta kubuta da rai da suka samu.
Bayan kwanaki takwas da suka ji kamar tsawon rayuwa ce, a ƙarshe sun isa sansanin 'yan gudun hijira na al Dabbah a Jihar Arewacin Sudan.
Abeer tana da shekaru 18, kodayake abin da ta fuskanta a tafiyar da ta kai kimanin kilomita 800 daga al Fasher ya riga ya sanya ta gwagwarmayar fiye da shekarunta.
Hanyar zuwa aminci ba ta da wani abu sai aminci. Mutane dauke da makamai sun dinga tsayar da motarsu akai-akai, suna bincike da wulakanta 'yan matan da ke tafiya tare da ita. "Sun yi mana barazana suna cewa: 'Za mu iya kashe ku.
Za mu iya yi muku fyade. Za mu iya barin ku a nan,' in ji Abeer, tana lura da cewa maharan sun din yi musu barazana.
"An ɗaure wata yarinya a kan bishiya na tsawon kwana uku a gabanmu. An yi wa kawarmu fyade kuma ta kasa magana bayan wannan jarrabawa."
Ga 'yara mata na Sudan,yakin ba a fagen daga kawai ake yin sa ba, ana yin sa ma a boye kullum a cikin gwagwarmayar juriya. PLAN International
A wani lokaci, motarsu ta lalace a cikin hamada, ta bar su a fili. An yi wa Abeer da 'yar uwarta duka aka kuma tilasta musu shan ruwa mai datti. Rashin komai a kusa da su bai ba su kariya ba—sai dai shiru kawai kake ji.
A ƙarshe, motar ta sake tashi ta yi sauri ta tura su zuwa sansanin al Dabbah, inda tanti da kayan aiki na yau da kullun suka ba dan kwanciyar hankali.
Amma Abeer ta ce ga mutane da yawa, wannan wahalar ba ta ƙare a nan ba—'yan matan da aka kai wa hari a yayin tafiya sun yi shiru, suna jin tsoron yin magana game da abin da suka fuskanta cikin bakin ciki.
"Ba za mu iya magana game da shi ba saboda muna jin tsoro. Waɗannan 'yan matan suna zaune tare da mu a nan a yanzu, har yanzu suna shan wahala."
Mariam ba ta yi sa'a ba—babu mota, babu gudu cikin sauri. Tsawon kwanaki biyar, ta yi tafiya a kan gonakin mutuwa, yayin da al Fasher ya faɗa hannun RSF.
Babu abinci. Babu ruwa. Sai dai sautin faɗa da ya mamaye al Fasher, da kuma gaggawar tserewa daga garin. Ta yi gudun hijira tare da iyalinta, tana ci gaba yayin da ƙarfinta ya ragu. Lokacin da suka isa sansanin 'yan gudun hijira, da kyar take iya tsaiwa.
Lokacin da mahaifiyarta ta kawo ta wani asibiti a sansanin, ta bayyana cewa yanayin Mariam ba wai kawai saboda gajiya ba ne - an yi mata fyaɗe. Binciken likita ya tabbatar da cewa tana da juna biyu.
Yanzu da aka raba ta da matsuguninta kuma ba ta da wurin zama mai kyau, Mariam da iyalinta suna fama da wahalar samun kulawar haihuwa, isasshen abinci mai gina jiki da ma mafi kyawun abubuwan buƙatar yau da kullum.
Yayin da yaƙin da ke tsakanin RSF da Sojojin Sudan ya shiga shekara ta huɗu a ranar 15 ga Afrilu, labarai kamar na Abeer da Mariam suna nan a ko'ina - amma ba kasafai ake jin su ba.
A faɗin Sudan, sama da mutane miliyan 12 sun rasa matsuguni, da yawa daga cikinsu a lokuta da dama. Duk biranen sun ɓace. Iyalai sun watse. Abin da ya rage shi ne ƙasar da babu tabbas game da rayuwa kuma kariya ba ta da yawa.
A cewar Plan International, 'yan mata da mata manya ne suka fi cutuwa daga rikicin.
Kimanin mutane miliyan 12 ne ke fuskantar barazanar cin zarafinsu, ciki har da fyade da cin zarafin mata. Waɗannan ba abubuwa ne da suka faru ba daban-daban, amma wani ɓangare ne na mummunan abin da ake maimaitawa a kan hanyoyi, a gidaje, da kuma cikin sansanonin da ake tsammanin akwai aminci.
A lokaci guda, tsarin da aka samar don taimaka wa waɗanda suka tsira yana rugujewa. An rusa ko kuma lalata asibitoci.
Wasu yanzu haka ana kai musu hari ta jiragen sama marasa matuƙa. An ci karfin ma'aikatan lafiya ko kuma ba za su iya isa ga waɗanda ke cikin buƙata ba.
Duk da haka, sannan duk da girman rikicin, yaƙin Sudan yana rasa kulawar duniya.
Ƙungiyoyin agaji, ciki har da Plan International, suna ci gaba da aiki a cikin mawuyacin hali don ba wa 'yan mata kamar Mariam da Abeer damar tsira. An kashe ma'aikatan agaji sama da 120 tun lokacin da rikicin ya fara.
Kuɗin tallafi ya yi ƙasa sosai, duk da ƙaruwar buƙatu. Sama da mutane miliyan 30 yanzu suna buƙatar taimakon gaggawa na jinkai.
"Muna buƙatar ƙarin tallafin jinkai. Ana iya cim ma wannan ne kawai ta hanyar ƙarin kuɗaɗen tallafi a lokacin da kasafin kuɗi na agaji ke raguwa.
Ba tare da tallafin kuɗi ba, rayuka - da makomar 'yan mata da matasa a faɗin Sudan - za su ɓace," in ji Mohamed Kamal, Daraktan Ƙasa na Plan International a tattaunawr sa da TRT Afrika.
Ga 'yan mata kamar Mariam, wannan na iya nufin tafiya dauke da ciki a lokacin gudun hijira, ba tare da isasshen kiwon lafiya ko aminci ba. Ga wasu, kamar waɗanda ke tafiya tare da Abeer, yanayin na nufin ɗaukar raunin da suke jin tsoron yin magana a kai.
Yaƙin kuma yana sace wani abu da ba a gani sosai, amma kuma yana da muni matuka: makomar al’uma.
Yara sama da miliyan 14 yanzu ba sa zuwa makaranta, yawancinsu 'yan mata ne. An mayar da ajujuwa sun zama tarkace ko kuma an mayar da su matsugunan 'yan gudun hijira.
Tare da dakatar da ilmantarwa, hatsari na ƙaruwa musamman ga 'yan mata: auren wuri, cin zarafi, da talauci wanda zai iya ɗaukar ƙarni da dama.
"Wannan rikici ya lalata Sudan. Matasa suna rasa ilimi, asibitoci sun lalace kuma ana wargaza al'ummomi. Za a ji sakamakon a dogon lokaci har tsawon karni da dama idan ba mu yi aiki yanzu ba," in ji Kamal.
Bincike ya nuna cewa a tsakanin 'yan matan da ba sa zuwa makaranta, ana ambaton aure a matsayin babban dalilin - wani sauyi da ke nuna yadda rikici ke sake fasalin ba kawai halin yanzu ba, har ma da yanayin rayuwa gaba daya.
"An katse mu daga samun ilimi," in ji Abeer. "Na daina karatu a aji shida." Mariam har yanzu tana da burin koma wa makaranta duk da cikin nata.
Shekaru uku bayan fara shi, rikicin ba waɗanda suka mutu ko suka gudu kawai ya siffantu da su ba, har ma waɗanda suka ci gaba da rayuwa da sakamakon da kawo marar kyau.
Ga 'yan matan Sudan, yaƙin ba wai kawai yaƙi ne a filin daga ba - ana ɗauke da shi a sirrance cikin yin shiru, ana tunani da kuma gwagwarmayar tsira da rayuwa.
Labarun Abeer da Mariam ba wai kawai shaidar asara ba ce. Suna tunatar da irin hatsarin da ake ciki idan duniya ta ci gaba da juya baya g warware rikicin.