Amurka da Iran sun yi musayar zazzafar kalamai gabannin shirin da Amurka ke yi na shelar sabbin takunkumai na tattalin arziki da za su iya tasiri kan Tehran da muhimman abokan cinikayyarta ciki har da China.
Yayin da yaƙin Amurka da Isra’ila kan Iran ya kusa kaiwa watanni shida, ɓangarorin biyu ba sa musayar wuta, amma ba sa tattaunawar zaman lafiya.
A wannan lokacin, jigilar mai ta Mashigar Hormuz ta tsaya kusan gabaɗaya yayin da Tehran ta rungumi wa ikon da take da shi ta hanyar barazanar kai hari kan ko wace tankar ai da ta yi ƙoƙarin wucewa ta tsukakkiyar hanyar ruwan.
Sakataren Ma’aikatar Kuɗin Amurka Scott Bessent zai gabatar da jawabi ga wani taron manema labarai da misalin ƙarfe 6.00 agogon GMT ranar Litinin cikin alƙawurrar bayyana "takunkumai mafi tsananni a tarihi" kan Iran yayin yake kira ga China ta haɗa kai da Washington.
China ce ke siyan fiye da kashi 80 na man da Iran ke fitarwa, in ji wasu ƙididdiga na shekarar 2025 daga kamfanin sarrafa bayanai na Kpler.
Beijing ta yi kira a bi diflomasiyya
Miamagana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran Esmaeil Baghaei ya bayyana ranar Asabar cewa shelar sabbin takunkuman Amurka kan Iran da ke tafe ta kasance "tabbatar da ikon mallakar ƙasa ta waje kan wata ƙasa mambar Majalisar Dinkin Duniya mai ‘yancin kai."
"Irin waɗannan takunkuman ba su da tushe a dokokin ƙasa da ƙasa," in ji shi a wani saƙon da ya wlalafa a shafin X.
Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya yi gargaɗi game da uƙuba ta tattalin arziki ga kowace ƙasa da ta samar da "kowace irin hanyar taimako ga Iran," ya cbayyana ranar Jumma'a cewa Washington tana sa ido kan "abin da ke faruwa" a rikicin.
"Za su so su yi yarjejeniya, amma a ganina ba su shirya yin yarjejeniyar da ta dace ba," in ji Trump game da Iran.
Zirga-zirgar Hormuz
Duk da cewa Amurka ta toshe hanyoyin jiragen ruwan Iran a tashoshin jiragen ruwanta, mashigar ruwa ta Hormuz ta ci gaba da kasancewa a rufe ga dubban matafiya ta ruwa da suka makale a kan daruruwan jiragen ruwa.
Jiragen ruwa guda hudu ne kawai suka wuce ta a mashigar ruwa ranar Alhamis, kuma babu daya daga cikinsu da ya kasnace babban jirgin ruwa mai jigilar ɗanye mai ko kuma babban jirgin ruwa ruwa mai jigilar iskar gas, kamar yadda bayanai suka nuna.
Sakataren Makamashin Amurka Chris Wright ya ce sojojin Amurka sun taimaka wajen jigilar miliyan 8 a rana ta mashigar cikin kwananki bakwai. Wannan ya ragu daga fiye da ganga miliyan 20 a kowace rana kafin yakin ko kuma kusan ɗaya daga cikin kowace ganga biyar da ake amfani da ita a duk duniya.
Hare-haren Amurka sun rage tattalin arzikin Iran sosai kuma sun lalata sojojin ruwanta da na sama, amma Tehran tana da isasshen karfin makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki don daƙile zirga-zirgar jiragen ruwa da kuma kai hari ga abokan hamayyarta na yanki.
A halin yanzu, Trump bai cim ma abin da ya tsara a farkon yaƙin ba irin na kassara shirin nukiliyar Iran - wanda har yanzu ba a tabbatar da halin da yake ciki ba saboda an hana masu binciken Majalisar Dinkin Duniya zuwa wurin tun shekarar 2025.
Hare-haren Amurka da Isra'ila a kan Iran sun kashe dubban mutane, ciki har da yaran makaranta Iran 168 a ranar farko ta yaƙin. Amurka ta ba da rahoton cewa fiye da sojoji 750 sun ji rauni sannan an kashe 18.
Iran ta ci gaba da nuna rashin tsoro
Babban hafsan sojin Iran, Manjo Janar Ali Abdollahi, ya yi alkawari a ranar Jumma'a cewa Iran za ta mayar da martani kan barazanar abokan gaba ta hanyar amfani da karfin soja, tare da daukar matakan "martani mai karya lagon abokan gaba, mai tsanani da kuma mai matukar barna."
Duk da haka, Shugaba Masoud Pezeshkian ya yi kira a nemi mafita ta hanyar diflomasiyya.
"Zai fi kyau a kawo karshen yaƙin a yau, yayin da muke da karfi da mutunci, kuma duniya baki daya ta amince da nasararmu tare da jaddada cewa Amurka, saɓanin dukkan dokoki, ta kai hari kan makarantunmu, asibitocinmu da kayayyakin more rayuwarmu, kuma ana kallonta da tsana a duniya," in ji Pezeshkian, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ISNA ya ruwaito.
Shugaban Majalisar dokokin Iran, Mohammad Baqer Ghalibaf—wanda shi ne babban wakilin kasar a tattaunawar sulhu da Amurka—ya amince cewa tattalin arzikin Iran na fuskantar matsin lamba, yayin da yake jawabi ga 'yan kasuwar Iran da Iraki a karshen ranar Alhamis.
"Ko ta yaya ƙarfin sojinmu yake, ba za mu iya tsira ba idan har mutane na fama da yunwa, kuma ba mu da musaya da zageyewar kuɗaɗe da ci gaban tattalin arziki, ko kuma samar da kayayyaki a cikin gida," in ji Ghalibaf, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na gwamnati, IRNA, ya ruwaito.

















