Dakarun rundunar yaƙi da ta’addanci ta musamman a Nijeriya sun yi nasarar kashe ‘yanta’addan ISWAP da wasu masu garkuwa da mutane dama a arewa maso gabashi da arewa maso yammacin Nijeriya.
Nasarar ta arewa maso gabashin ƙasar ta faru ne yayin da ‘yanta’addan ISWAP suka yi yunƙurin kai hari kan sansanin dakarun Operation Hadin Kai a Magumeri da sanyin safiyar Alhamis 7 ga watan Mayu.
Wata sanarwa da jami’an watsa labaran Opertaion Hadin Kai, Laftanar Kanal Sani Uba ya fitar ta ce duk da cewa ‘yanta’addan sun kutsa wasu sassa na katangar sansanin, dakarun sun mayar da martani kuma sun daƙile harin ‘yanta’addan inda suka kashe gommai daga cikinsu.
“Yana da muhimmanci a bayyana cewa bincike a kewayen ya nuna layukan ɗigar jini mai tsawo da na jan jiki da kuma gawarwakin ‘yanta’adda, lamarin da ya tabbatar da yawan mace-mace da aka samu a cikin maharan yayin da harin da suka kai ya gaza samun nasara,” in ji sanarwar.
“Kazalika dakarun sun ƙwace makamai da harsasai daga ‘yanta’addan da ke tserewa ciki har da bindiga mai sarrafa kanta ta harbo jirgin sama ƙirar PKT da bindigogi ƙirar AK 47 da kuma gidajen harsasai,” a cewar Uba.
Sai dai kuma sanarwar ta ce sojoji biyu sun rasa rayukansu a fafatawar yayin da wani hafsa da sauran jami’an da suka ji raunuka suke samun kulawa a halin hanzu.
Kazalika sanarwar ta ce wasu kayayyaki sun lalace yayin yaƙin inda wasu gine-gine na wucin-gadi suka kama da wuta yayin musayar wutar.
Dakaru sun kashe ‘yanta’ada a jihar Zamfara
A wani labarin makamancin haka kuma dakarun runduna ta musamman da ke yaƙar masu tayar da ƙayar baya a arewa maso yammacin Nijeriya, Operation Fansan Yamma sun kashe ‘yanta’adda tare da ƙwace makamai daga gare su a jihar Zamfara.
Wata sanarwar da jami’in watsa labaran rundunar Operation Fansan Yamma, Lutanan Kanal Aliyu Danja, ya fitar ta ce lamarin ya faru ne yayin da dakarun suka fita sintirin yaƙi da ‘yanbindiga a ƙananan hukumomin Kauran Namoda da Birnin Magaji na jihar Zamfara.
Sanarwar ta ce sintirin da aka ƙaddamar domin hana ‘yanbindigan sakat ya ci karo da su a ƙauyen Doumbourum inda aka yi musayar wuta tsakanin sojoji da ‘yan bindigan.
“Dakarun masu jarumtaka sun buwayi ‘yanta’addan da ƙarfin wuta da ya fi nasu, lamarin da ya tilasta wa masu aikata laifukan tserewa a gigice bayan sun samu mace-mace… a cikinsu,” in ji sanarwar.
Bayan arangamar, sanarwar ta ce, dakaru sun samu sun kassara ‘yanta’adda uku tare da ƙwace makamai ciki har da wata bindiga ɗaya ƙirar AK-47, da bindiga mai jigida ɗaya da bindiga ɗaya da aka ƙere a gida da kuma gidajen harsasay 7 tare da harsasai 571.
Bugu da ƙari sanarwa ta ce ba samu mutuwa ko ɗaya cikin dakarun ba yayin aikin.










