Isra’ila ta yi shelar matakin karɓe iko da wani waje mai tarihi a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan

Hukumomin Isra’ila suna shirin ƙwace ɓangare mai yawa na Sebastia, wani wuri mai muhimmanci a fannin kimiyyar binciken kayan tarihi a yankin da aka mamaye, kamar yadda wasu takardu suka nuna.

By
Isra’ila ta ƙwace wuri mai yawa a yankin Sebastia inda ake binciken kimiyya na kayan tarihi kusa da Nablus Gaɓar Yamma Da Kogin Jordan

Isra’ila tana shirin ƙwace waje mai yawa a wani wuri na tarihi a Gaɓar Yamma Da Kogin Jordan, in ji wasu takardun gwamnati, kuma tuni ‘yan kama-wuri-zauna suka kafa wani sansani cikin dare, duk da cewa ƙasar tana fuskantar matsin lamba na daƙile hare-haren ‘yan kama-wuri-zauna a cikin Falasɗinu.

Hukumar Fararen Hula ta Isra’ila ta ayyana burinta na ƙwace wuri mai yawa a Sebastia, wata muhimmiyar cibiya ta binciken kayan tarihi a Gaɓar Yamma Da Kogin Jordan, kamar yadda aka bayyana a cikin wata takardar da kamfanin dillancin labaran AP ta samo ranar Alhamis.

Ƙungiyar Peace Now, wadda ke fafatukar hana tsugunar da ‘yan kama-wuri-zauna, ta bayyana cewa wurin ya kai kimanin kadada 200 — wanda ya zama ƙwace mafi girman da Isra’ila ta yi.

Matakin ya zo ne yayin da Isra’ilawa ‘yan kama-wuri-zauna suka yi bikin samar da sabon wurin zama da ba a ba da iznin kafa shi ba kusa da Bethlehem, kuma wani lauya Bafalasɗine ya bayyana cewa an kama wani mai fafatuka a Gaɓar Yamma Da Kogin Jordan,  kuma an kai shi asibiti.

Sai dai kuma, ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta Human Rights Watch ta ce ta yi wa Isra’ila ta aikata laifukan yaƙi a lokacin da ta kori Falasɗinawa 32,000 daga sansanonin ‘yan gudun hijira uku daga Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da ƙarfin tuwo a bana.

Isra’ila za ta ƙwace maje mai tarihi

Umarnin Isra’ila wadda ta bayar ranar 12 ga watan Nuwamba ya bayyana filayen da take son ta ƙwace a yankin Sebastia. Ƙungiyar Peace Now, wadda ta miƙa takardun ga AP, ta ce wurin binciken kimiyya na kayayyakin tarihi, inda dubban bishiyoyin zaitun suke, na Falasɗinawa ne.

Waje ne da Kiristoci da Musulmai suka yi imanin cewa a nan aka binne Annabi Yahaya.

Isra’ila ta yi shelar shirye-shiryen gina wajen a matsayin wani wajen yawon buɗa ido a shekarar 2023.

An riga an fara tone-tone kuma gwamnatin ta ware fiye da kuɗin shekel miliyan 30 ( dala miliyan $9.24) domin gina wajen, in ji ƙungiyar Peace Now da kuma wata ƙungiyar fafatukar ‘yancin ɗan’adam ta daban.

Umarnin ya bai wa Falasɗinawa wa’adin kwanaki 14 su ƙalubalanci matakin.

Ɓangare mafi girma na filin da Isra’ila ta ƙwace a baya ya kai (kadada 70 ) a Susya, wani ƙauye a kudancin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye, kamar yadda ƙungiyar Peace Now ta bayyana.

’Yan kama-wuri-zauna sun ƙaddamar da wani sabon matsuguni da ya saɓa wa doka

‘Yan Isra’ila ‘yan kama-wuri-zauna sun ce sun kafa wani matsugunni da ba a ba da izinin kafawa ba kusa da Bethlehem.

Shugaban ƙungiyar ‘yan kama wuri zauna na Etzion, Yaron Rosenthal, ya yi maraba da matsugunnin.

Sabon matsugunnin na kusa da wata hanya mai cike da hada-hada inda a ranar Talata aka caka wa wani ɗan Isra’ila wuƙa har ya mutu.

Hamas ba ta ɗauki alhaƙin kai harin ba, amma a cikin wata sanarwa ta kira shi “wani martani na al’ada da ake yi wa yunƙunrin mai mamaya na ɗaiɗaita gwagwarmayar Falasɗinawa,” tana mai shan alwashin cewa zaluncin Isra’ila ba zai gudana ba ba tare da an ƙalubalance shi ba.

Hagit Ofran, Daraktar Shirin Ƙungiyar Peace Now na sa ido kan kama wuri zauna, ta ce  matsugunin na kan wani wuri da a aka sansanin sojin Isra’ila ne. Hotunan da ‘yan kama wuri zauna suka wallafa a kan intanet sun nuna gidajen wucen gadi a wurin da kuma motocin buldoza da ke aiki a wurin.

Isra’ila ta ƙwace Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Gabashin Birnin Ƙudus da Gaza — wuraren da aka ware wa Falasɗinawa domin gina ƙasarsu a nan gaba — a yaƙin shekarar 1967. Ta tsugunar da fiye da Yahudawa 500,000 a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, yawancinsu a matsugunoni ba bisa ƙa’ida ba, ciki har da fiye da ‘yan kama wuri zauna 200,000 a Gabashin Birnin Ƙudus.

Gwamnatin Isra’ila tana da ‘yan adawa masu tsatssaurar ra’ayin ‘yan mazan jiya da yawa da ke goyon bayan kama-wuri-zauna, ciki har da ministan kuɗi Bezalel Smotrich, wanda yake tsara manufofin kama-wuri-zauna da kuma Minista Itamar Ben-Gvir, wanda ke kula da rundunar ‘yan sandan ƙasar.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya nuna damuwa kan rikici na baya bayan nan da Isra’ilawa ‘yan kama-wuri-zauna suka haddasa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye.

"Ina fatan ba zai kasance haka ba," kamar yadda Rubio ya shaida wa manema labarai kwanan nan, a lokacin da aka tambaye shi kan ko abubuwan da suka faru a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye za su iya barazana ga tsagaita wuta a Gaza.

"Ba ma tsammanin zai haddasa haka. Za mu yi komai da za mu iya yi domin tabbatar da cewa bai faru ba."