‘Yanta’adda sun kai hari wani ofishin ‘yansanda a arewa maso gabashin Nijeriya a ranar Asabar, inda suka kashe ‘yansanda huɗu, sannan kuma suka kai hari wani sansanin ‘yan gudun hijira, kamar yadda rundunar ‘yansanda ta bayyana, a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar ƙaruwa a hare-haren ta’addanci.
‘Yansandan sun ce “ana zargin ‘yanta’addan mambobin Boko Haram/Daesh ne suka kai hari hedikwatar ‘yansandan Nganzai da nufin kwace garin”, wanda ke ƙasa da kilomita 100 arewa da Maiduguri, babban birnin jihar Borno a arewa maso gabas.
Kimanin makonni biyu da suka gabata, ‘yan ƙunar baƙin-wake uku sun tayar da bama-bamai a wata kasuwa mai cunkoso da wasu wurare a Maiduguri, inda suka kashe aƙalla mutane 23, a ɗaya daga cikin hare-hare mafi muni da aka gani a birnin cikin shekaru.
Jami’an tsaro da ke bakin aiki a harin na ranar Asabar “sun gwabza da maharan a wani mummunan artabu”, kamar yadda kakakin ‘yansanda ya bayyana a wata sanarwa, amma “jami’an ‘yansanda huɗu” sun mutu.
Wata ƙungiyar ‘yanta’adda kuma ta kai hari wani wurin tsaro a ƙofar sansanin da ke karɓar ‘yan gudun hijira a Damasak, kusa da iyakar Nijar.
‘Yanta’addan sun kashe ɗan ƙungiyar bijilanti, sannan suka ƙone kimanin bukkoki 20 waɗanda aka yi da ciyawa, kamar yadda ‘yansanda suka ce.
A cikin hare-haren biyu, ‘yansanda da sojoji tare da ‘yan sa-kai na fararen hula “sun mayar da martani cikin gaggawa tare da fatattakar maharan”, in ji sanarwar ‘yansanda.
‘Yan ta’addan Boko Haram da ƙungiyar Daesh mai adawa da ita sun ƙara yawan hare-hare kan sojoji, ‘yansanda da fararen-hula a watannin baya-bayan nan, yayin da Nijeriya, ƙasa mafi yawan jama’a a Afirka, ke fama da rikicin ‘yan tayar da ƙayar baya wanda aka jima ana fama da shi.














