Matsanancin talauci yana raguwa a Ghana – Hukumar Ƙididdiga
A cikin watanni uku kacal fiye da mutum 360,000 ne suka fita daga cikin ƙangin talauci tsakanin watannin Yuli zuwa Satumba na shekarar 2025.
An samu raguwar talauci a faɗin ƙasar Ghana duk cewa har yanzu akwai tazara mai yawa ta fuskar samun kuɗin shiga tsakanin jama’ar ƙasar, kamar yadda wani rahoto kan talauci mai taken Quarterly Multi-Dimensional Poverty Index (MPI) ya bayyana.
A cikin watanni uku kacal fiye da mutum 360,000 ne suka fita daga cikin ƙangin talauci tsakanin watannin Yuli zuwa Satumbar shekarar 2025.
Hukumar Kididdiga ta Ghana (GSS) ta ce tsakanin watan Afrilun shekarar 2024 zuwa watan Maris ɗin shekarar 2025 mutum 950,000 ne suka fita daga matsanancin talauci — wato an samu raguwa da kaso 24.9 cikin 100 na talauci a shekarar 2024, sai raguwar da aka samu da kaso 21.9 cikin 100 na talauci a shekarar 2025.
A gefe guda, mutanen da suke rayuwa cikin matsakanin talauci sun ragu daga mutum miliyan 8.1 zuwa mutum miliyan 7.2 tsakanin watan Yunin shekarar 2024 zuwa ƙarshen watan Satumba shekarar 2025.
Ba kuɗin shiga kawai alƙaluman MPI suke dubawa ba, suna duba yanayin rayuwar mutum da kiwon lafiya da ilimi da aikin yi da sauransu. Sannan alƙaluman suna ayyana iyali a matsayin matalauci ne idan ya kasa cim ma kaso ɗaya cikin uku da alƙaluman da ake dubawa.
Kiwon lafiya da yanayin da mutum yake rayuwa su ne abubuwan da suka fi muhimmanci wajen duba yawan talakawan da ƙasa take da su, waɗannan abubuwa biyu su ne suke da kaso 76.9 cikin 100 na abin da ake dubawa yayin da ilimi yake da kaso 13.4, sai sana’a ko aiki wanda ke da kaso 12.3.