Golan Barcelona ya ƙi karɓar kyautar gwarzon wasa

Garcia yana cewa, “Yawan tare ƙwallo da na yi ba abin kirki ba ne. Ba abin yin murna ba ne idan ya zama sai na yi ta tare ƙwallo da yawa haka.”

By
Joan Garcia ya koka kan rashin kyawun 'yanwasan baya na Barcelona. / Reuters

A maraicen Litinin ne Barcelona ta samu rashin nasara a karo na biyu a jere, inda a wannan karon Girona ta doke ta da ci 2-1 a wasansu na mako na 24 a gasar La Liga ta 2025/26.

Wannan rashin nasara ta janyo babbar abokiyar hamayyar Barca, wato Real Madrid ta ɗare saman teburin La Liga, inda ta bai wa Barca tazarar maki biyu.

A makon jiya ne Atletico Madrid ta lallasa Barcelona da ci 4-0 a gasar Copa del Rey, a wani wasa da aka sallami golan na Barca a minti 85 na wasan.

Wannan raunin tagomashi da ya faɗa kan ƙungiyar, ya sa Garcia na ganin cewa ba zai yi murnar ayyana shi a matsayin gwarzon wasa a wasan da suka sha kaye a hannun Girona ba.

Gabanin wasan, Barcelona na jan ragamar La Liga da fifikon maki guda kan Real Madrid. kuma a wasan, Garcia ya nuna bajinta matuƙa wajen tare hare-haren zura ƙwallo a ragarsa, don neman nasara.

Sai dai a ƙarshe, ƙwallo biyun da aka zura a ragarsa ce ta bai wa Girona nasara. Wannan ya fusata Garcia, inda ya koka kan rashin nuna ƙoƙari daga wajen masu tsaron bayan Barca, da kuma alƙalan wasa.

Yamal ya zubar da ɗurme

A dai wasan ne, tauraron ɗanwasan gaban Barcelona, Lamine Yamal ya ɓarar da bugun ɗurme da ya samu a mintunan ƙarshe na zagayen farko na wasan, sanda ana 0-0.

Bayan dawowa hutun rabin lokaci, Barca ta zura ƙwallo ta hannun ɗanwasan baya, Pau Cubarsi, sai dai mintu biyu bayan haka, sai Thomas Lemar na Girona ya rama ƙwallon.

Sai a minti na 86, ɗanwasan Girona, Fran Beltran ya ci ƙwallo ta biyu, wanda ke nufin duk ƙoƙarin da Garcia ya yi na tare ƙwallaye ba su yi babban tasiri ba.

Mai shekaru 24, Garcia ya jaddada cewa, kasancewar ya yi ta aikin tare ƙwallo wata alama ce ta raunin ‘yan-bayan tawagar da Hansi Flick ke jagoranta. Don haka ƙididdigar yawan tare ƙwallo ba abin alfahari ba ce.

Ya ce, “Mun yi ta samun hare-hare, cikin sauƙi ake cin mu. Yawan tare ƙwallo da na yi ba abin yabo ba ne. Ba abin yin murna ba ne idan ya zama sai na yi ta tare ƙwallo da yawa haka.”