| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Buɗaɗɗiyar maƙabartar Gaza: Gawawwaki 8,000 sun maƙale, yayin da aikin kwashe ɓaraguzai ya tsaya cak
Sama da Falasdinawa 8,000 ne har yanzu ba a gani ba a ƙarƙashin tan miliyan 68 na baraguzai, yayin da ƙoƙarin fito da su ke fuskantar ƙarancin kayan aiki da kuma fargabar sabbin hare-hare.
Buɗaɗɗiyar maƙabartar Gaza: Gawawwaki 8,000 sun maƙale, yayin da aikin kwashe ɓaraguzai ya tsaya cak
Ma'aikatan gine-gine sun fito da wata gawa Bafalasɗine daga cikin ɓaraguzai, a wani gida da Isra'ila ta kai hari / Reuters

Fiye da watanni shida bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta shiga tsakani don dakatar da yaƙi, Gaza ta kasance wata ƙatuwar maƙabarta da ba a san iyakarta ba.

A cewar Hukumar Kare Fararen Hula ta Gaza da kuma wani rahoto na kwanan nan na jaridar Haaretz, aƙalla Falasdinawa 8,000 ne suka rage a maƙale a ƙarƙashin baraguzan gidajensu.

Duk da yarjejeniyar tsagaita wutar, sake gina yankin bai kankama ba, inda ƙasa da kashi ɗaya cikin ɗari na tan miliyan 68 na baraguzan aka kwashe zuwa yanzu.

Girman barnar da aka yi yana da wuyar siffantawa.

Wani binciken haɗin gwiwa da Majalisar Ɗinkin Duniya, Bankin Duniya, da Tarayyar Turai suka gudanar ya ƙiyasta cewa kwashe ɓaraguzan kawai zai ci kuɗi sama da dala biliyan 1.7.

Alexander De Croo, Shugaban Shirin Ci Gaban Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP), ya tabbatar da cewa idan aka ci gaba da tafiya a hakan, za a ɗauki aƙalla shekaru bakwai kafin a kwashe duka ɓaraguzan yankin.

Wannan ƙalubale na sufuri ya ƙara riƙidewa sakamakon kasancewar nakiyoyin da ba su tashi ba da kuma gawarwakin dubban mutane da ke ruɓewa a wurin.

‘Takardu da Tsayawar Aiki’

Ga iyalai da dama a Gaza, jiran ba wai kawai jinkiri ba ne na tsarin gwamnati.

Ƙungiyoyin kare farar hula sun ci gaba da karɓar dubunnan kiran waya daga dangi waɗanda suka san ainihin wurin da gawarwakin masoyansu suke.

Sai dai kuma, ƙarancin manyan injuna da kayan aiki na musamman ya sa an dakatar da aikin tuno gawarwaki a wasu yankunan da aka fi yi wa barna, ciki har da unguwannin Shujaiyeh da Tuffah na birnin Gaza.

A yawancin lokuta, gawarwakin suna can ne bayan layin da ake kira (Yellow Line) — yankunan da har yanzu kai-tsaye suke ƙarƙashin ikon sojojin Isra’ila.

Ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa kamar Red Cross da Majalisar Ɗinkin Duniya sun gaya wa iyalai cewa dole ne a sami amincewar ɓangaren Isra’ila kafin a kwashe gawarwakin, tsarin da yawancin lokaci yake karewa ba tare da nasara ba.

Yarjejeniyar tsagaita wuta tana cikin barazana

Jinkirin farfaɗo da yankin yana zuwa ne yayin da keta yarjejeniyar tsagaita wuta ta watan Oktoban 2025 da Isra’ila ke yi kullum ta dagula lamarin.

Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta ba da rahoton cewa Isra’ila ta kashe Falasdinawa 828 tun bayan fara tsagaita wuta, wanda hakan ya ƙara yawan mutanen da aka kashe zuwa sama da 72,000 daga kisan ƙiyashin da aka shafe shekaru biyu ana yi.

Wannan ci gaba da kai hare-hare da Isra’ila ke yi ya tsorata ma’aikatan ceto da ’yankwangilar ƙasa da ƙasa daga hci gaba da ayyukansu, yayin da wuraren kare farar hula da motocin ɗaukar marasa lafiya ke ci gaba da kasancewa cikin hatsarin hare-hare.

Ko a wuraren da za a iya gudanar da aikin ma, lamarin yana cike ce-ce-ku-ce.

A Rafah, iyalai a yankin sun yi zanga-zanga kwanan nan kan wasu kamfanonin kwangila, inda suke zargin su da yin haɗin gwiwa da hukumomin Isra’ila don kwashe wuraren domin gina gidaje ba tare da izinin dangi da aka yi wa rasuwa ba.

Ga mutane da dama, kula da waɗannan gawarwaki ba aiki ne kawai na sufuri ba, a’a, lamari ne na haƙƙin ɗan’adam.

Kamar yadda wani mazaunin wurin ya bayyana: “Mutane suna da haƙƙin a san sunayensu, a binne su, kuma a yi musu makoki.”

Rumbun Labarai
Amurka da Iran sun amince su kawo ƙarshen yaƙi. Amma akwai wanda za a iya cewa ya yi nasara?
Trump ya sanar da cim ma yarjejeniyar Iran mai tarihi, ya yi alƙawarin buɗe Mashigar Hormuz nan-take
Yarjejeniyar Amurka da Iran ta ƙunshi sake buɗe Hormuz, taƙaita aikin nukiliya: babban jami'i a Iran
An gano wani dutse mai ɗauke da rubutun sunan Khalifa Umar ibn Khattab a Madina
Iran ta kai hare-hare manyan cibiyoyin sojin Amurka 18 a Kuwait da Bahrain yayin da hankula ke tashi
Amurka ta kai hare-hare da dama ta sama Iran yayin da hankula suka tashi kan sake ɓarkewar yaƙi
Helikwaftan sojin Amurka ya faɗi kusa da Mashigar Hormuz; matuƙansa suna 'lafiya', in ji Trump
Ƙungiyar Houthi ta yi barazanar haramta wa Isra'ila jigilar kayayyaki a Bahar Rum gaba ɗaya
Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare a faɗin Iran yayin da yaƙin Gabas Ta Tsakiya ya sake ɓarkewa
Iraniyawa sun nuna juriya da ƙalubale irin na lokacin yaƙi a wani gagarumin gangami a Tehran
Fashe-fashe sun girgiza tsibirin Qeshm na Iran yayin da Kuwait ta tare jerin makamai masu linzami
Iran ta ce ta kai hari kan wani jirgi mai alaƙa da Amurka da Isra'ila bayan hari kan wani jirginta
Iran ta dakatar da tattaunawa da Amurka saboda hare-haren Isra'ila a Lebanon: rahoto
Iran ta kai hari sansanin sojin Amurka a Kuwait bayan hari kan benen sadarwar Hormozgan
Masar ta yi kira ga kwamitin tsaro na MƊD ta dakatar da faɗaɗa [harin] da Isra'ila ke yi a Lebanon
Iran ta ci gaba da aikin samar da gas a wurarenta uku na South Pars da ke cikin teku
Netanyahu ya kira taron gaggawa bayan Hezbollah ta kai hari na ban mamaki ga sojin Isra'ila
Zaman jiragen sojojin Amurka ya janyo wa filin jirgin saman Ben Gurion na Israila asarar $248M
Dakarun Juyin-Juya-Hali na Iran sun ce sun kai hari sansanin Amurka na sama a Kuwait
Amurka ta kai sabbin hare-hare a wuraren soji a kudancin Iran — rahoto