Farashin fetur a Amurka ya yi tashin gwauron zabi inda ya kai dala 4 kan kowanne galan, a cewar ƙungiyar masu motoci ta AAA, yayin da a gefe guda Iran ta ce tana fafatawa da Amurka kuma “babu gudu-babu ja da baya” kana ɓangarorin biyu sun tsananta kai hare-hare.
Kazalika ‘yan Houthi na ƙasar Yemen sun bayyana cewa za su sanya takunkumin teku ga Saudiyya da kuma kayayyakin makamashi da take fitarwa ta hanyar mashigar Bab al Mandab.
Hauhawar farashin na nuna barazanar siyasa da Shugaban Amurka Donald Trump ke fuskanta kafin babban zaɓe na tsakiyar wa'adinsa a watan Nuwamba, inda batun tsadar rayuwa ke zama babban abin damuwa ga masu kaɗa ƙuri'a.
Farashin man ya zarce matakin da aka samu a watan Maris bayan yaƙin Amurka da Isra’ila kan Iran ya sanya Tehran mayar da martani ta hanyar rufe Mashigar Hormuz- wata muhimmiyar hanyar jigilar makamashi ta duniya.
Kazalika an samu hauhawar farashin mai a duniya sakamakon yaƙin, lamarin da ya sanya farashin gas na Amurka ya ƙaru.
Rabon da a samu irin wannan hauhawar farashin man, tun a shekarar 2022 inda ya zarce dala 4 kan kowanne galan, sakamakon yaƙin Rasha kan Ukraine.
A bara farashin matsakaicin galan ɗin gas da ake amfani da shi yau da kullum ya kai dala 3.14.
A 'yan makonnin nan, masu sayan mai a Amurka sun samu sauƙi na ɗan lokaci bayan matsi da iyalai da dama suka shiga - man ya sauka zuwa kasa dala 4 kan kowacce galan sakamakon yarjejeniyar wucin daɗi tsakanin Washington da Tehran.
Komawa zuwa matsayin kafin 9 ga Yuli
An sake komawa yaƙin bayan lokacin.
A tsawon shekaru, iyalai a Amurka sun fuskanci ƙarin farashin mai, haka kuma mummunan tashin farashin makamashi a wannan shekarar ya haifar da ƙarin da ba a taɓa gani ba a cikin shekaru uku.
A ranar Litinin Iran ta bayyana cewa tana yaƙi “babu ƙaƙƙautawa” da Amurka, yayin da Washington ke faɗaɗa kai hare-harenta a Iran.
A nata martanin, Tehran, ta ci gaba da kai hare-hare a yankin, galibi kan ƙawayen Amurka da sansanoninsu na a yankin Gulf.
A yanzu dai, ana sa ran Ministan Harkokin Cikin Gida na Iran Eskandar Momemi zai je babban birnin Pakistan da ke shiga tsakani a ranar Litinin, a cewar wata majiya daga Pakistan.
Haka kuma, Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran ya faɗa a ranar Litinin cewa ana ci gaba da musayar ra'ayoyi ta diflomasiyya da Amurka - ta hanyar masu shiga tsakani.
Rufe mashigar Bab al Mandab
Ana sa ran farashin makamashi na duniya zai yi tashin gwauron zabi bayan sanarwar ƙungiyar Houthi ta Yemen kan sanya takunkumin teku ga Saudiyya, wanda ke barazana ga ikon babbar ƙasar da ke fitar da mai zuwa ƙetare ta Mashigar Hormuz da Bab al Mandab.
Idan aka yi nasara, wannan mataki zai kara kawo cikas ga kasuwar makamashi ta duniya wadda ta fuskanci gagarumin tsaiko sakamakon yadda Iran ta rufe Mashigar Hormuz da kuma rufe tashoshin jiragen ruwa na Amurka da ke Iran.
Bab al Mandab babban hanya ce a duniya wadda ke tsakanin Yemen a yankin Larabawa da Djibouti da Eritrea da ke yankin Kusurwar Afirka, wanda ya haɗa Bahar Maliya, Aden da kuma Tekun Indiya.
Sannan rufe mashigar zai shafi kasuwannin duniya waɗanda suka dogara da Saudiyya - babbar ƙasar da ke fitar da ɗanyen mai a duniya, wadda ke samar da ganga miliyan 10 a kowace rana - don shigo da makamashinsu.


















