Shugaban Burkina Faso, Ibrahim Traoré, ya jagoranci bikin yaye matasa 65,000 da suka kammala horon kishin ƙasa na dole da ƙasar ta kafa, inda ya yi kira a gare su da su yi aiki tukuru domin kare martaba da cikakken ikon ƙasarsu.
Gwamnatin Traoré ta ƙaddamar da shirin horon kishin ƙasa na dole a shekarar 2025, wanda ya wajabta wa ɗaliban da suka kammala sakandare shiga horo na tsawon wata guda. Horon ya mayar da hankali kan koyar da kyawawan ɗabi’un zama ɗan ƙasa, haɗin kan ƙasa, ladabi da tarihin ƙasar. Bayan kammala horon, ana ba su takardar shaidar kammalawa, wadda ake buƙata domin samun gurbin shiga jami’a.
Shugaban Burkina Faso ya kuma buƙaci matasan da su rungumi tawali’u da kishin ƙasa, tare da fahimtar yadda duniya da siyasar ƙasashen duniya ke gudana.
“Mutumin da ba shi da ilimi haɗari ne ga juyin juya halinmu,” in ji Traoré yayin bikin yaye daliban a ranar Alhamis, kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasar ta bayyana.
“Ko da wane irin hali kuka tsinci kanku a ciki, dole ne ku ƙara ƙoƙari kuma ku zarce abin da ake tsammani daga gare ku… Ku guji bin ɓarauniyar hanya ko neman mafita mai sauƙi, domin irin wannan hanya tana kaiwa ga cin amana,” in ji shi ga matasan Burkina Faso.
Wannan shi ne rukuni na biyu na waɗanda suka kammala wannan shirin horo na dole, wanda hukumomi suka ce an ƙaddamar da shi ne domin ƙarfafa haɗin kan al’umma da kuma gina sabon ƙarni na ’yan ƙasa masu jajircewa da kishin ƙasarsu.





















