Somaliya ta rage lokutan aiki a ofisoshin gwamnati saboda azumin watan Ramadan

A ‘yan shekarun nan tsarin aikin ma'aikata na Somaliya ya kasance abin muhawarar jama'a, musamman game da yawan kwanaki da sa'o'in aiki.

By
Bisa ga jadawalin watan Ramadan da aka yi wa kwaskwarima, ana sa ran ma'aikatan gwamnati za su yi aiki na kimanin awanni 30 a kowane mako a Somaliya. / Reuters

Ma'aikatar Kwadago da Harkokin Jama'a ta Somaliya ta sanar da rage lokutan aiki a hukumance a lokacin watan Ramadan mai alfarma, hakan na bisa ga tsarin ayyukan kwadago da aka daɗe ana yi a ƙasar wadda ke da mafi yawan al’ummar Musulmai.

A cikin wata sanarwa da ta fitar bayan watan ya kankama, ma'aikatar ta isar da gaisuwa ga ma'aikatan Somaliya da kuma al'ummar Musulmi baki ɗaya, tana mai sauyi da aka samu ya nuna muhimmancin watan Ramadan da kuma buƙatar sassautawa ma'aikata masu yin azumi.

A ƙarƙashin tsarin da aka yi wa kwaskwarima, ofisoshin gwamnati za su yi aiki daga ƙarfe 9:00 na safe zuwa 3:00 na yamma, inda aka sanya awanni shida a ranakun aiki ga ma'aikatan gwamnati.

Matakin na da nufin rage yawan aiki da ake gudanarwa yayin da za a ci gaba da muhimman ayyukan gwamnati.

Kodayake, ana sa ran kamfanoni masu zaman kansu za su ci gaba da gudanar da ayyukansu a lokutan da aka saba, amma akwai yiwuwar wasu ‘yan kasuwa suma su iya samar da wani tsari na lokaci mai sauƙi.

Za a rufe wuraren cin abinci

A lokacin Ramadan, gidajen cin abinci da yawa suna rufewa da rana, inda wasu ke rufewa na tsawon watan baki ɗaya, wasu kuma da daddare kawai suke buɗewa don samar da abinci buɗe baki na azumi.

A 'yan shekarun tsarin aikin ma’aikata na Somliya ya kasance batun muhawarar jama'a, musamman game da yawan kwanaki da sa'o'in aiki.

An ware Juma'a a matsayin ranar hutu a cikin mako a hukumance , yayin da ma'aikata da dama ke aiki a ranakun Asabar da Lahadi.

Bisa ga jadawalin watan Ramadan da aka yi wa kwaskwarima, ana sa ran ma'aikatan gwamnati za su yi aiki na kimanin awanni 30 a mako, ko da yake ya danganta da tsarin hutu ko wacce ma’aikata.

Wannan tsarin da aka gabatar ba zai yi aiki a lokaci ɗaya a dukkan fannoni na ma’aikatun ƙasar ba.

Jami'an Sojojin Ƙasa na Somaliya, waɗanda ke ci gaba da fafatawa da Al-Shabaab, da kuma ma'aikatan lafiya a cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnati da na masu zaman kansu, za su iya ci gaba ko kuma tsawaita lokaci bisa ga yanayin tsarin aiki da ke sauyawa saboda buƙatu.