Rundunar sojin Nijeriya sun yi nasarar dakile wani shirin satar man fetur tare da kama mutum 14 da ake zargi da fasa bututu a yankin Lekki Free Zone da ke kusa da matatar mai ta Dangote a Jihar Legas.
Sojojin sun kai wannan samame ne da misalin ƙarfe 1:30 na dare a ranar 16 ga Afrilu, 2026, bayan sun samu ingantattun bayanan sirri kan ayyukan ɓata-garin.
A lokacin samamen, an kama waɗanda ake zargin dumu-dumu suna tsiyayar man fetur ba bisa ƙa’ida ba, kamar yadda wata sanarwa da Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Runduna ta 81, Laftanal Kanar Musa Yahaya ta fitar ta bayyana.
Sanarwar ta ci gaba da cewa masu laifin sun haɗa wani dogon bututu daga can tsakiyar teku zuwa wata motar dakon mai (tanka) da suka ɓoye ta a cikin daji, sannan suna amfani da injin famfo mai amfani da janareta don tura man cikin motar.
Da ganin sojojin sun nufo su, waɗanda ake zargin sun yi ƙoƙarin tserewa, amma zaratan sojojin da ke aikin sa-ido sun yi maza sun ci ƙarfinsu tare da kama su duka.
Abubuwan da aka ƙwato a wurin sun haɗa da: Motar tanka maƙare da man fetur ɗin da aka sato da mota SUV kirar Lexus Highlander mai lamba APP 67 JQ Lagos da motar daukar kaya kirar Ford Hilux mai lamba BY 117 FST Lagos.
Sai injin famfo guda ɗaya da kuma injin jirgin ruwa mai ƙarfin 40HP. Kazalika an ƙwato bututun roba masu yawa irin wanda ake amfani da su a masana’antu da sauran kayan aikin fasa bututu.
A halin yanzu, waɗanda ake zargin da kayayyakin da aka kama suna tsare a hannun Runduna ta 81 don gudanar da binciken farko, kafin a miƙa su ga hukumomin da suka dace don gurfanar da su gaban shari’a kamar yadda doka ta tanada.
A karshen sanarwar rundunar sojin Nijeriya ta sake jaddada aniyyarta ta yaƙi da satar danyen mai da sauran ayyukan zagon ƙasa ga tattalin arziƙin ƙasa, musamman a wuraren da ke da muhimman ababen more rayuwa na ƙasa.








