| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Sojojin Nijeriya sun kama mutum 14 da ake zargi da satar mai a Jihar Legas
A lokacin samamen, an kama waɗanda ake zargin dumu-dumu suna tsiyayar man fetur ba bisa ƙa’ida ba, kamar yadda wata sanarwa da Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Runduna ta 81, Laftanal Kanar Musa Yahaya ta fitar ta bayyana.
Sojojin Nijeriya sun kama mutum 14 da ake zargi da satar mai a Jihar Legas
Sojojin Nijeriya sun kama wasu da ake zargi da satar mai a jihar Legas / Nigerian army

Rundunar sojin Nijeriya sun yi nasarar dakile wani shirin satar man fetur tare da kama mutum 14 da ake zargi da fasa bututu a yankin Lekki Free Zone da ke kusa da matatar mai ta Dangote a Jihar Legas.

Sojojin sun kai wannan samame ne da misalin ƙarfe 1:30 na dare a ranar 16 ga Afrilu, 2026, bayan sun samu ingantattun bayanan sirri kan ayyukan ɓata-garin.

A lokacin samamen, an kama waɗanda ake zargin dumu-dumu suna tsiyayar man fetur ba bisa ƙa’ida ba, kamar yadda wata sanarwa da Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Runduna ta 81, Laftanal Kanar Musa Yahaya ta fitar ta bayyana.

Sanarwar ta ci gaba da cewa masu laifin sun haɗa wani dogon bututu daga can tsakiyar teku zuwa wata motar dakon mai (tanka) da suka ɓoye ta a cikin daji, sannan suna amfani da injin famfo mai amfani da janareta don tura man cikin motar.

Da ganin sojojin sun nufo su, waɗanda ake zargin sun yi ƙoƙarin tserewa, amma zaratan sojojin da ke aikin sa-ido sun yi maza sun ci ƙarfinsu tare da kama su duka.

Abubuwan da aka ƙwato a wurin sun haɗa da: Motar tanka maƙare da man fetur ɗin da aka sato da mota SUV kirar Lexus Highlander mai lamba APP 67 JQ Lagos da motar daukar kaya kirar Ford Hilux mai lamba BY 117 FST Lagos.

Sai injin famfo guda ɗaya da kuma injin jirgin ruwa mai ƙarfin 40HP. Kazalika an ƙwato bututun roba masu yawa irin wanda ake amfani da su a masana’antu da sauran kayan aikin fasa bututu.

A halin yanzu, waɗanda ake zargin da kayayyakin da aka kama suna tsare a hannun Runduna ta 81 don gudanar da binciken farko, kafin a miƙa su ga hukumomin da suka dace don gurfanar da su gaban shari’a kamar yadda doka ta tanada.

A karshen sanarwar rundunar sojin Nijeriya ta sake jaddada aniyyarta ta yaƙi da satar danyen mai da sauran ayyukan zagon ƙasa ga tattalin arziƙin ƙasa, musamman a wuraren da ke da muhimman ababen more rayuwa na ƙasa.

MAJIYA:Nigerian army
Rumbun Labarai
Shugaba Tinubu na Nijeriya na halartar taron Afirka da Faransa a Kenya
Rundunar Sojin Nijeriya ta musanta kashe fararen-hula a harin sama a jihar Neja
Nijeriya da Amurka sun ƙarfafa haɗin gwiwa kan tsaro da yaƙi da ta’addanci bayan ganawa a Washington
Sojin Nijeriya sun halaka ‘yanta’adda 50, sun yi asarar dakaru biyu yayin daƙile harin ISWAP a Yobe
'Yanbindiga a Nijeriya sun kashe mata masu juna biyu uku da wasu mutum 11 a Filato
Dakarun sojin Nijeriya sun kashe 'yanta'addan ISWAP da masu garkuwa da mutane
Sojojin Nijeriya sun ceto yaran da aka sace daga gidan marayu
Sanƙarau ta kashe mutum 33 a Sokoto yayin da hukumomi ke ƙoƙarin daƙile yaɗuwarta
Dangote ya sanar da shirinsa na samar da megawat 20,000  na wutar lantarki a Nijeriya
Nijeriya da Amurka sun ƙaddamar da cibiyoyin aikin tsaro don magance matsalar rashin tsaro
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda a Jihar Zamfara
Nijeriya na nuna kayan tsaro da ta ƙera a taron baje-kolin SAHA 2026 da ke gudana a Istanbul
Kwamitin wucin-gadi na Majalisar Dokokin Nijeriya zai je Afirka ta Kudu kan batun ƙyamar baƙi
Jam'iyyar NDC ta miƙa takarar shugaban ƙasa ga kudancin Nijeriya, in ji Buba Galadima
Nijeriya za ta fara kwaso 'yan ƙasar daga Afirka ta Kudu saboda rikicin ƙyamar baƙi
Peter Obi ya bayyana shirin ficewa daga jam'iyyar ADC
Ba mu yanke shawara kan makomarmu ta siyasa ba – Kwankwaso
Sojojin Nijeriya sun lalata maɓoyar 'yan Boko Haram a Sambisa, sun kashe 'yan ta'adda masu yawa
An kama 'yan Nijeriya 62 a Uganda kan zargin gudanar da coci ba bisa ƙa'ida ba
Dakarun Nijeriya sun kashe ‘yan ta’adda 18 a arewa maso-gabas, in ji rundunar soji