Musayar harbe-harben bindiga ta ɓarke a kusa da ofishin jakadancin Isra'ila na Istanbul, wanda ke gundumar Beşiktaş. An daƙile 'yan bindiga uku da ake zargi, sannan an jikkata 'yansanda biyu, kamar yadda Ministan Cikin Gida na Turkiyya ya sanar ranar Talata.
Ministan, Mustafa Ciftci ya ce waɗanda ake zargin sun buɗe wuta kan 'yansanda a wajen ginin Yapi Kredi Plaza, wanda ya janyo musayar harbi, inda aka "kawar" da duka maharan uku. 'Yansandan da suka jikkata sun samu raunuka marasa muni.
Ministan Shari'a, Akin Gürlek ya ce masu shigar da ƙara sun ƙaddamar da bincike nan-take, kan rahotannin da aka samu tun da fari na harbe-harben bindiga a yankin, inda aka aika mataimakin mai shigar da ƙara da masu shigar da ƙara biyu.
Gwamnan Istanbul, Davut Gül, ya ce ofishin jakadancin Isra'ila da ke cikin ginin plazar, a rufe yake tsawon shekaru biyu da rabi.
Gano mahara da alaƙoƙinsu
An gano su waye maharan da ake zargin, kuma ana bincike kan alaƙoƙinsu. An kuma gano cewa wani Yunus E.S, wanda aka kama shi a mace, yana da alaƙa da wata ƙungiyar ta'addanci da ke amfani da addini.
Sai kuma sauran mahara biyu an kama su da raunuka, wato Onur C. da Enes C., waɗanda 'yan-uwan juna ne. Shi kuma Onur C yana da rakod ɗin laifukan ƙwaya, cewar Ma'aikatar harkokin cikin gida.
"An kuma gano sadarwar dijital mai faɗi tsakaninsu ukun, kuma ana ci gaba da binciken masu raunin da ake zargin," cewar Ma'aikatar.
Jami'ai sun ce ana gudanar da bincike tare da haɗin kan jami'an tsaro, don ƙoƙarin bankaɗo cikakken ƙudurin maharan da girman shirinsu na kai hari














