Babban hafsan sojin Mali ya ce an kashe sojoji kusan 30 a fafatawar da aka yi don kwato babban garin Anefis da ke yankin arewacin ƙasar daga hannun 'yanta'adda masu alaƙa da Al Qaeda da kuma 'yan a-waren Abzinawa.
Ƙungiyar ta 'yan a-waren ƙabilan Abzinawa, ta ƙwace garin Anefis a ranar 4 ga Yuli a jerin hare-haren da ta kai ƙasar da ke Yammacin Afirka.
Ko da yake, 'yanta'addan ba su kai ga ƙwace sansanin sojoji a garin ba sakamakon jibge sojoji da mayaƙan sa-kai daga rundunar sojojin Afirka ta Rasha a yankin har sai da aka ƙara tura wasu ƙarin sojojin.
A ranar Jumma’a ne sojojin suka ce sun sake ƙwace Anefis bayan kusan mako guda ana fafatawa.
Dakaru sittin sun jikkata
"Ina mai baƙin cikin rasa kusan dakaru 30, shahidai 30. Sannan muna da kusan dakaru 60 da suka jikkata, ciki har da waɗanda yanayinsu ya yi muni," kamar yadda babban hafsan sojin Mali, Janar Jean Elysee Dao ya shaida ta kafar talbijin na ƙasar.
Sojojin Mali sun ce sun kama 'yanta'adda "kimanin 100".
Garin Anefis na da nisan kilomita 100 daga birnin Kidal mai muhimmanci, wanda 'yantawayen suka ƙwace a wani hari da suka kai a watan Afrilu, inda suka kashe Ministan Tsaron Mali Sadio Camara.














