Shugaban rundunar tsaron Amurka ya bayyana cewa Amurka na fuskantar ƙarancin makamai masu mahimmanci sakamakon yaƙi mai tsada da take yi da Iran.
A wani rahoto irinsa na farko da aka gabatar wa Majalisar Dokokin ƙasar, hukumar sa ido kan ma’ikatar tsaron Amurka, Pentagon, ya bayyana cewa tsakanin 28 ga Fabrairu zuwa 30 ga Yuni, rundunar Operation Epic Fury (OEF) ta kashe kimanin dala biliyan 33.4, da kuma dala biliyan 22.3 da aka kashe kan makamai a tsakanin wannan lokacin kawai.
Rahoton ya kuma bayyana cewa "kuɗaɗen da aka kashe kan ayyukan rundunar OEF sun jawo da ƙarancin kayayyaki masu mahimmanci kuma sun nuna matsalolin da masana'antu ke fuskanta wajen samar da makamai."
Hukumar ta bayyana irin gagarumar asarar kayan aiki masu yawa da jiragen yaƙin Amurka da aka yi a lokacin yaƙin, inda ta rubuta cewa jiragen yaƙin F-15 guda huɗu sun lalace, sai wani jirgin yaƙin F-35 da ya yi hatsari da kuma wasu manyan jiragen ruwa guda bakwai masu cike da mai na KC-135 da suka lalace, sannan an harbo jiragen sama marasa matuƙa na MQ-9 Reaper guda 30.
Asarar jiragen ruwa
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da damuwar da ake nunawa game da ƙarancin makaman.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social a ranar Litinin, Trump ya jaddada cewa masana'antun Amurka suna samar da "makamai masu inganci kana na musamman fiye da kowane lokaci a tarihinmu."
Sai dai duk da hakan, rahotanni sun nuna cewa ƙarancin makamai masu linzami masu cin dogon zango da kuma makamai masu kakkaɓo jiragen sama maras matuƙa sun taƙaita shirin soji kan Iran, inda sojojin Amurka suka yi amfani da kusan kashi 80 cikin 100 na makamansu masu kakkaɓo jiragen yaƙi na THAAD.
A cikin sa'o'i 24 da aka soma yaƙin, Rundunar Tsaro ta Amurka (CENTCOM) ta kai hare-hare kan wurare fiye da 1,000 - hare-haren da ba ta maimaita irinsu ba a tsawon watannin da suka biyo baya.
Hukumar sa idon ta ƙara da cewa hare-haren Iran sun lalata ɗaruruwan wurare a faɗin cibiyoyin Amurka a Kuwait da Bahrain da Qatar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Saudiyya da Iraƙi da Oman da kuma Jordan.
An cire waɗannan kuɗaɗe na sake gina wuraren daga cikin kasafin kuɗin da ake sa ran yi, yayin da jami'ai ke tantance ko za a sake gina wuraren da suka lalace da kuma waɗanda za su ba da kuɗin gudanar da ayyukan.




















