Kotu ta ɗaure wata Bajamushiya kan fashi da makami da tsakar rana a DR Congo

Honorine Porsche ta shaida wa kotu cewa ta saci kuɗin da ake zargin sun ɓace amma daga baya ta shaida wa kotun cewa jami’an tsaro da suka kutsa bankin ne suka ƙwace kuɗin daga gare ta.

By
A ranar 17 ga Oktoba, da kusan tsakiyar rana, an kewaye wani reshen RawBank a tsakiyar Kinshasa da jami'an tsaro bayan an kai masa hari.

An yanke wa wata Bajamushiya wadda ‘yar asalin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ce hukuncin shekaru 10 a gidan yari a ranar Laraba a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo saboda yunƙurin fashi da makami da tsakar rana a wani banki.

Honorine Porsche, mai shekaru 37, ta bayyana a gaban kotun soji a babban birnin ƙasar Kinshasa inda kotun ta same ta da laifin fashi da makami.

A ranar 17 ga Oktoba, da kusan tsakiyar rana, an kewaye wani reshen RawBank a tsakiyar Kinshasa da jami'an tsaro bayan an kai masa hari.

An samu ruɗani wanda ya ɗauki awanni da dama, kafin a kama mutane biyar ciki har da Porsche a cikin ginin. Babu wanda ya ji rauni.

A cewar bankin, kuɗaɗe daidai da kimanin dalar Amurka 20,000 sun ɓace a kuma ba a gano kuɗin ba.

A lokacin shari'ar, tun da farko Porsche ta ce ita ce ta saci kuɗin, amma ta bayyana cewa daga baya wasu jami'an tsaro da suka kutsa bankin ne suka ƙwace kuɗin daga gare ta.

Fushin jama'a a kafafen sada zumunta

Bayan kama matar, an ga matar 'yar Jamus a wasu bidiyo da aka wallafa a kafafen sada zumunta inda aka ganta rabin jikinta tsirara, inda aka ga wasu jami'an tsaro suna taɓa ta. Hotunan sun haifar da fushin jama'a a DRC.

Porsche ta ƙi magana a kotu a ranar Laraba, inda ta faɗa wa kamfanin dillancin labarai na AFP a lokacin da take fita daga ginin cewa ba ta da "ƙarfin magana".

Keno Grade, wanda shi ne ƙaramin jakadan Jamus a Kinshasa, wanda ya halarci kotun zaman kotun, ya ƙi yin magana kan batun.

Lauyan Porsche ya bayyana cewa Porsche na da niyyar ɗaukaka ƙara.