| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
Turkiyya ta umarci makarantu su goge hotunan ɗaliban da aka wallafa ba tare da izinin iyaye ba
Umarnin ya buƙaci makarantu su duba shafukan intanet da na sada zumunta, tare da cire abubuwan da suka wallafa da ke dauke da hotunan dalibai ko bayanan sirri.
Turkiyya ta umarci makarantu su goge hotunan ɗaliban da aka wallafa ba tare da izinin iyaye ba
Wannan ɗabi'a ta jawo suka a yanar gizo saboda damuwa kan cewa hakan na take sirrin ɗalibai.

Ma'aikatar Ilimi ta Turkiyya ta umarci makarantu a faɗin ƙasar su cire hotuna da bidiyoyi na ɗalibai da ake iya samunsu a bainar jama'a har sai an samu izinin iyaye, a matsayin wani sabon mataki da aka ɗauka don ƙarfafa kare bayanan sirri.

Umarnin ya buƙaci makarantu su duba shafukan intanet da na sada zumunta, tare da cire abubuwan da suka wallafa da ke ɗauke da hotunan ɗalibai ko bayanan sirri.

Ma'aikatar ta ce za a ɗauki mataki na shari'a kan duk wanda aka samu da laifin wallafa hotunan ɗalibai ba tare da izini ba ko kuma amfani da su ba yadda ya dace ba.

An kuma umarci ma'aikatan makaranta su kammala horon wajibci kan kare bayanan sirri da tsaron bayanai.

Wannan umarni ya zo ne a daidai lokacin da wasu malamai a Turkiyya suka tara mabiya da yawa a shafukan sada zumunta irin su Instagram, TikTok da YouTube ta hanyar wallafa abubuwan da ke faruwa a aji da ke nuna ɗalibai, abin da ya janyo hankalin miliyoyin masu kallo.

Wannan ɗabi'a ta jawo suka a shafukan intanet saboda damuwa kan cewa hakan na keta dokar kare sirrin ɗalibai.

An samu irin wannan ƙorafin a wasu wurare. A Sifaniya, malaman makaranta da ƙwararru kan shari'a sun yi suka ga ɓullowar abin da aka kira “TeachTokers” waɗanda ke amfani da hotunan ɗalibai da hulɗar aji don tallata kansu.

Umarnin Ma'aikatar Ilimi ta Turkiyya ya zo ne yayin da kamfanonin fasaha da hukumomin da ke tsara dokoki ke fuskantar ƙarin bincike game da sirrin shafukan intanet.

A makon jiya, kamfanin Meta ya janye wani sabon fasalin AI da ya ƙaddamar a Instagram wanda ke bai wa masu amfani da shi damar ƙirƙirar hotuna ta hanyar amfani da abubuwan da ke cikin sauran shafukan jama’a, bayan shan suka kan batun sirri da neman izini.

Kafin a cire shi, an sanya masu shafukan Instagram kai-tsaye su amince ba tare da izininsu ba domin yin amfani da hotunansu da ake samu a fili don ƙirƙirar hotunan AI ko gyara su ba tare da sanin su ko samun takamaiman izini ba.

Daga bisani Meta ya ce ya yi “kuskure” kuma ya bayyana cewa an cire wannan “damar”.