| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Kotu ta yi wa mutum uku ɗaurin shekara 10 a Nijeriya kan safarar makamai
Ɗaurin na zuwa ne a daidai lokacin da wata mata, Halima Haliru Umar, wadda jami’an hukumar DSS suka kama, ta amsa laifin samunta da harsasai 302 a gaban wata babbar kotun Tarayya a Abuja.
Kotu ta yi wa mutum uku ɗaurin shekara 10 a Nijeriya kan safarar makamai
Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ne suka gurfanar da mutanen a gaban kotu / Reuters
awa ɗaya baya

Babbar kotun majistire ta ɗaya mai zama a Jalingo, babban birnin jihar Taraba a Nijeriya, ta yi wa mutum uku ɗaurin shekara 10 ba tare da zaɓin tara ba bayan ta same su da laifin safarar makamai.

Gidan talabijin na gwamnatin Nijeriya (NTA) ya ruwaito cewa hukumar tsaron ƙasar ta farin kaya (DSS) ce ta gurfanar da Sakina Garba da Ali Gono da kuma Ibrahim Abdulrashid a gaban kotu bayan an kama su tsakanin watan Janairu da watan Fabrairun shekarar 2026.

Ɗaurin na zuwa ne a daidai lokacin da wata mata, Halima Haliru Umar, wadda jami’an hukumar DSS suka kama, ta amsa laifin samunta da harsasai 302 a gaban wata babbar kotun Tarayya a Abuja.

Kama mutanen a jihar Taraba ya zo ne bayan bayanan sirri da suka tona asirin shirinsu na safarar makamai daga ƙauyen Bantaje a ƙaramar hukumar Wukari, jihar Taraba, domin kai wa wani ƙasurgumin mai garkuwa da mutane.

NTA ya ruwaito cewa majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an kama mutanen ne a kan hanyar Wukari zuwa Jalingo tare da makaman da suka ɓoye cikin buhunan abinci.

"An kama mutanen da buhunan abinci biyu inda suka ɓoye bindiga ƙirar AK-47 ɗaya, da harsasai 984 masu tsawon 7.6mm da kuma harsasai 105 masu tsawon 7.82mm. Kazalika an samu gidan harsasan AK-47 guda 14 a cikin buhunan da na’urar POS guda uku da kuma kuɗi N200,200 " in ji majiyar da NTA ya ambato.

Kazalika gidan talabijin ɗin ya ruwaito cewa a gaban babbar kotun tarayyar ta Abuja bayan jami’an DSS sun gabatar da harsasan 302 da suka samu a hannun wadda ake zargi da safarar makaman, Halima Umaru, sai ta amsa laifin tuhumar da aka yi mata.

Daga nana sai alƙalin kotun, mai sharia Haywa Joseph Yilwatda ya ɗaga zaman kotun zuwa ranar 8 ga watan Mayu domin yanke mata hukunci.

Daga farko dai shaidan DSS ya bayyana yadda aka kama wadda ake zargin a jihar Filato yayin da take riƙe da harsasai 302 wadda take kan hanyar kaiwa ga wani babban mai garkuwa da mutane da ya yi ƙurin suna.

Ya gabatar da harsasan da rahoton bincike da kuma kudin da aka karɓe daga gare ta.