Sarkin Morocco ya jaddada aniyar ƙasarsa ga haɗin kan Afirka
Wasu magoya bayan Senegal sun yi yunkurin shiga filin wasa bayan da aka dauki matakin buga fenareti.
Sarkin Maroko Mohammed VI a ranar Alhamis ya ce kyakkyawar alakar Afirka za ta ci gaba da ɗorewa bayan abin da ya kira “mummunar” halayyar da ta kawo tarnaƙi a mintuna na karshe na wasan final a Gasar AFCON 2025 tsakanin Maroko da Senegal.
'Yan wasan Senegal sun fice daga filin wasa don nuna rashin amincewa da hukuncin da na’urar VAR ta bayar kafin su koma su doke mai masaukin baƙi Morocco da ci 1-0 bayan ƙarin lokaci a ranar Lahadi.
Ƙungiyoyin magoya bayan Senegal sun yi karo da jami'an tsaron Maroko yayin da suke ƙoƙarin shiga filin wasa bayan hukuncin bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Senegal ta daɗe tana ɗaya daga cikin ƙawayen Maroko na kusa a Afirka, inda kamfanonin Maroko da bankuna suka faɗaɗa jari a cikin 'yan shekarun nan, wanda hakan ya ƙarfafa tasirin diflomasiyyar masarautar.
Awanni bayan kammala wasan karshen, kafofin sada zumunta a ƙasashen biyu sun kasance cikin tashin-tashina.
Wasan ya fuskanci "abubuwan takaici" da "halaye marasa daɗi," in ji Sarkin a cikin wata sanarwa da ya fitar a fadarsa.
"Da zarar karsashi da kishin ƙwallon sun lafa, 'yan’uwantaka tsakanin Afirka za ta ci gaba da yin nasara," in ji shi.
Ya ƙara da cewa, "Babu abin da zai iya kawo cikas ga dangantakar da ke tsakanin al'ummominmu na Afirka na tsawon ƙarni, ko kuma haɗin gwiwa mai amfani da aka gina da ƙasashe a faɗin nahiyar kuma aka ƙarfafa ta hanyar haɗin gwiwa mai ƙarfi."
Gasar ta kuma nuna cigaban Maroko kuma ta wakilci "nasara ga dukkan Afirka," in ji shi.
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) ta ce za ta ɗauki "matakin da ya dace" bayan ta yi bitar abubuwan da suka faru a wasan, yayin da shugaban FIFA Gianni Infantino ya yi Allah wadai da ɗabi'ar 'yan wasan Senegal da mambobin tawagar masu horarwa.