| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
5 minti karatu
Isra’ila ta tafka asarar biliyoyin dala a yaƙin kwanaki 12 da Iran
Masana sun yi gargaɗin cewa tattalin arzikin Isra’ila ka iya nakasa, sannan rashin aikin yi zai iya ƙaruwa kuma yawanmasu fama da fatara ka iya ƙaruwa idan aka ci gaba da rikicin.
Isra’ila ta tafka asarar biliyoyin dala a yaƙin kwanaki 12 da Iran
Giɓin kasafin kudin Isra’ila ya ƙaru da kashi shida cikin 100, in ji masana. / AA

Tattalin arzikin Isra’ila ya fuskanci koma-baya sakamakon yaƙin kwanaki 12 da Iran inda kuɗaɗen da suka salwanta sakamakon yaƙin suka kai biliyoyin daloli, in ji rahotannin kafafen watsa labarai da kuma masana.

Isra’ila ta kashe kimanin dala biliyan 5 a cikin makon farko na kai hare-hare kan Iran, in ji kafar intanet ta Financial Express , yayin da kuɗin da take kashewa kullum a kan yaƙin ya kai dala miliyan 725, inda take amfani da dala miliyan 593 wajen kai hare-hare kuma take ajiye dala miliyan 132 wa matakan tsaro da kuma tattara sojoji.

Jaridar The Wall Street Journal ta ba da rahoton cewa kuɗin da ake kashewa kan tsarin tsaron saman makamai masu linzami ya kama daga dala miliyan 10 zuwa dala miliyan miliyan 200 a Isra’ila a ko wace rana.

Da jumullan kuɗin yaƙin ya kai dala biliyan 12 idan hare-haren sun ci gaba har zuwa wata ɗaya, in ji cibiyar nazarin manufofin tattalin arziki na Aaron Institute for Economic Policy da ke Isra’ila.

Naser Abdelkarim, wani mataimakin farfesa a Jami’ar Amurka ta Falasɗinu, ya ce hare-haren ba su yi tasiri kai tsaye kan kuɗin da Isra’ila ke kashewa kan soji ba kawai, amma sun ƙara yin tasiri kan harkar ƙera kayayyakin ƙasar, yana mai cewa, idan aka yi la’akari da tasirin kai tsaye da akashin hakan, yaƙin ka iya sa Isra’ila ta rasa abin da ya kai dala biliyan 20.

Abdelkarim ya ce ana tsammanin giɓin kasasfin kuɗin Isra’ila zai ƙaru zuwa kashi 6 cikin 100, kuma kuɗin diyya ga ‘yan ƙasar da lamarin ya shafa zai sake ta barɓare harkar kuɗin ƙasar.

Adadin ‘yan Isra’ila da ke ƙauracewa daga gidajensu a makon farko ya zarce 10,000, kuma ‘yan ƙasar 36,465 sun nemi a biya su diyya, in ji hukumar harajin Isra’ila.

Abdelkarim ya ce gwamnatin Isra’ila na tunanin ɗaukar ɗaya daga cikin matakai uku domin cike giɓin kasafin kuɗi da ke daɗa ƙaruwa: rage kuɗin da gwamnati za ta kashe kan kiwon lafiya da ilimi ko ƙara haraji ko kuma aron kuɗi, wanda zai iya ƙara yawan bashin ƙasar idan aka kwatanta da kuɗin shiga da sama da kaso 75 cikin 100.

Ma’aikatar kudin Isra’ila ta bayyana cewa kuɗaɗen ƙasar na yanzu na raguwa cikin sauri, kuma ta nemi a tura dala miliyan 857 zuwa ma’aikatar tsaro, yayin da ta kuma nemi a rage dala miliyan 200 cikin kasafin kuɗin ma’aikatun lafiya da ilimi da ayyukan a’ulluma.

Jaridar tattalin arziƙin Isra’ila Globes ta ba da rahoton cewa yawancin waɗannnan kuɗaɗen za a yi amfani da su ne wajen biyan kuɗaɗen sojoji.

An gayyaci wasu sojojin ko ta kwana 450,000 zuwa bakin aiki a wani ɓangare na matakan tanadi na yaƙin.

Abdelkarim ya bayyana cewa darajar kuɗin sehekel na Isra’ila ya faɗi zuwa 3.7 ga dalar Amurka, amma ta sake murmurewa zuwa shekel 3.5 ga dala, yana mai cewa karyewar darajar dala da kuma cinikin dala bisa hasashe sun taka rawa wajen ‘yar darajar da shekel ɗin ta sake samu.

Fargabar masu zuba jari na tasiri kan tattalin arzikin Isra’ila

Masana sun yi gargaɗin cewa yanayin ci gaban tattalin arzikin Isra’ila zai iya raguwa, inda rashin aikinyi ka iya ƙaruwa kuma yawan fatara ka iya ƙaruwa idan yaƙin ya ci gaba.

Iran ta kai hare-hare kan muhimman ababen more rayuwa a Tel Aviv da Haifa, ciki har da wani hari da ya hana aiki a Bazan, matatar mai mafi girma a Isra’ila, lamarin da ke janyo asarar dala miliyan 3 a ko wace rana, in ji jaridar Financial Times.

Filin sauƙa da tashin jiragen sama na Ben Gurion  ya dakatar da aiki sakamakon hare-haren ramuwar gayyar Iran. Filin jiragen na samun sauƙa da tashi jirage 300 da matafiya 35,000 a ko wace rana, kuma sai ranar Lahadi ne filin ya fara ƙwarƙaryar aiki domin mayar da wasu mutane. Katsewar [aikinta] ka iya sanadiyyar asarar tattalin arzikin mai yawa.

Rufe filin sauƙa da tashin jirage da ya fi girma ƙasar ya zo daidai ne da lokacin da kamfanin jiragen Isra’ila, El Al, ya dakatar da jigilar matafiya da kuma juya akalar jirage domin kauce wa barazanar afka musu.

An juya akalar wani jirgi da ke tafiya birnin Paris a kan hanya kuma ya sauƙa a ɓangaren Cyprus da Girka ke iko da shi, kuma wanda ke tafiya Bangkok ya sauƙa a Roma a ala tilas.

Asarar gudanarwa da aka samu a wannan lamarin kawai ta kai kimanin dala miliyan 6.

Kasuwanni ma sun yi asara sakamakon tsananin tashin hankalin na soji kamar yadda makamai masu linzamin Iran suka afka wa kasuwa musayar  lu’ulu’un Isra’ila, wani fanni da darajarsa ya kai kashi 8 na jummular ababen da Isra’ila ke fitarwa.

Cibiyar nazarin harkar lu’ulu’u na Isra’ila ta ce hare-haren sun tayar da damuwa game da kasuwar musayar hannayen jari ta Tel Aviv.

Tasirin lamarin kan hannayen jari ya gigita masu zuba jari, lamarin da ya sa wasu suka sayar da hannayen jarinsu kuma ya gaggauta komabayar kasuwa, wadda kuma, ta yi barazana ga lafiyar tattalin arziƙi na ƙanƙanin lokaci