| Hausa
WASANNI
4 minti karatu
Ina Mo Salah zai koma daga Liverpool?
Zaman Mohamed Salah a Liverpool ya kasance ɗaya daga cikin lokuta mafi ɗaukaka a tarihin ƙwallon ƙafar Ingila, in ji masharhanta.
Ina Mo Salah zai koma daga Liverpool?
Mohamed Salah ya shirya domin barin Liverpool a cikin watan Mayu. / Reuters / Reuters
30 Maris 2026

Zaman Mohamed Salah a Liverpool ya kasance ɗaya daga cikin lokuta mafi ɗaukaka a tarihin ƙwallon ƙafar Ingila, in ji masharhanta.

Ya zura ƙwallaye 255 a raga cikin shekaru tara tare da ɗaukar kofuna takwas. Wannan ɗaya ne daga cikin mafi ɗaukaka a cikin tarihin ƙwallon ‘yanwasa da aka taɓa gani a fagen ƙwallon ƙafar Ingila.

Mohamed Salah zai bar Liverpool a ƙarshen wannan kakar. Yayin da yake shirin tafiya, bari mu yi dubi ga abin da ya yi da kuma yadda makomarsa take. Ya fara ne daga Nagrig, wani ƙaramin ƙauye a Masar.

Baiwarsa da basirarsa sun kai shi ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea. Amma sun yi amfani da shi ne kawai na lokaci ƙalilan. Ya koma buga wasannin aro a Fiorentina da Roma, kuma a nan ne duniya ta san da shi.

Roma ba su so barin sa ya tafi ba, amma Liverpool ta dage. A lokacin zafin shekarar 2017, koci Jürgen Klopp ya biya fam miliyan £34 a kansa. Wannan matakin ya sauya tarihin ƙwallon ƙafa.

Kakarsa ta farko? ƙwallaye 44 a cikin dukkan gasanni. Wani tarihi cikin gasar Firimiya na wasanni 38. Amma Salah ba mai ba da mamakin kaka ɗaya ba ne kawai. Ya ci gaba da ƙoƙari babu ƙaƙƙautawa akai-akai.

Lambobi mafi yawa

Ya zura ƙallaye 20 ko fiye da haka a raga a cikin ko wace daga cikin kakar wasa takwas a jere, wani abin da babu wani ɗanwasan Liverpool da ya taɓa yi.

Ya kai ga ƙwallaye 100 gabannin ko wane ɗanwasa a tarihin kulob ɗin – cikin wasanni 151. Kuma kofunan sun zo da su: Kofin Gasar Zakarun Turai na shekarar 2019, Kofin Gasar Lig ta farko da ƙungiyar ta ci cikin shekaru 30 a shekarar 2020, sai kuma kofin Caraboa guda biyu da kofin duniya na kulob-kulob da kuma kofin Super Cup na UEFA ɗaya.

Ranar 24 ga watan Mayu, filin wasan Anfield zai yi bankwana da ɗaya daga cikin manyan taurarin ƙwallon ƙafa na Afirika.

A kakar da ta gabata a shekarar da Arne Slot ya kama aiki a kulob ɗin, ya ba da lambobi da suka fi yawa a tarihin wasansa – ƙwallaye 29 da taimakawa wajen zura ƙwallo a raga 18 – kuma ya sake ɗaukar kofin gasar Firimiya.

Sau uku yana lashe kyautar ɗanwasan da ya fi iya murza leda, ya samu kyautar takalmin zinari sau huɗu; Salah ya kasance ɗaya daga cikin ‘yanwasan da suka fi ƙwarewa a wannan lig ɗin.

Ƙungiyoyin da zai iya komawa

Kuma yayin da yake shirin barin kulob din a watan Mayu, ya ce: "Ban taɓa tunanin cewa wanna kulob ɗin, wanna birnin da waɗannan mutanen za su iya zama wani ɓangare na rayuwata sosai haka ba. Liverpool ba ƙungiyar ƙwallon ƙafa ba ce kawai. Matuƙar ƙauna ce. Tarihi ne. Wani ruhi ne." 

To yanzu ina zai koma? Ba a tabbatar da wata ƙungiya ba tukunna. Amma ana sonsa kuma ana nemansa daga ko ta ina. Saudiyya ce ke kan gaba. Al-Ittihad ta yi ƙoƙarin siyansa a shekarar 2023 kan kuɗi fam miliyan £150, kuma Liverpool ta bayyana hakan.

Amma a yanzu babu wata yarjejeniya a kansa, kuma rahotanni sun ce suna sake bibiyarsa. Al-Hilal da Al-Nassr ma suna ciki. Idan yana son ya tsaya a Turai, PSG da Barcelona ma zaɓi ne a gare shi.

Masharhanta sun kuma ambato zakarun Lig ɗin Turkiyya Galatasaray a cikin masu nemansa .

Kuma akwai ƙungiyar Gasar Lig ɗin Amurka. Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta San Diego FC, ta wani attajiri ɗan Birtaniya ɗansalin ƙasar Masar Mohamed Mansour, wadda ba ta ɓoye son ɗanwasan ba.

Ko ma me zai biyo baya, babu shakka kan abu ɗaya: a matsayinsa na mai shekara 33, Mohamed Salah na da ƙarin ƙwallon ƙafa da yawa tare da shi.