Ghana na shirin gina tashar makamashin nukiliyarta ta farko

Ghana tana shirin fara shiga harkar makamashin nukiliya inda take niyyar fara gina tashar nukuliyarta ta farko daga shekarar 2027 domin faɗaɗa hanyoyin samun makamashi a ƙasar.

By
Ghana na ƙoƙarin faɗaɗa hanyoyin samun lantarkinta ta hnayar gina tashar makamashin nukiliya / Others

Ghana tana shirin kasancewa cikin ƙasashen Afirka da ke da makamashin nukiliya inda take ƙoƙarin fara gina tasharta ta nukiliya ta farko.

Ministan ma’aikatar makamashi,  Dokta Robert Sogbadji, ya bayyana wurare biyu da za a yi amfani da su - ɗaya a lardin Yammacin ƙasar kuma ɗaya a lardin Tsakiyar Ƙasar, domin samar da wata babbar masana’anta da wata ƙaramar masana’anta, a wani ɓangare na matakin faɗaɗa hanyoyin samun makamashin ƙasar.

"Muna da ɓangarori biyu da aka ayyana inda muke son mu saka sabuwar tashar makamashin nukiliyarmu. Wani wuri zai karɓi babbar tashar makamashi yayin da ɗaya wurin zai karɓi ƙaramar tashar makamahin nukiliyar a wani  kewaye na masana’antu," in ji shi.

Sogbadji ya bayyana cewa gwamnatin ta fara ɗaukar matakai na siyan filaye domin ayyukan.

An fara shirye-shorye, amma ba a bayyana abokin ginin ba

Da yake magana a lokacin bikin karramawa na makamashi na Ghana karo na 9, Dokta Robert Sogbadji ya tabbatar da cewa an fara ayyukan shirye-shirye ciki har da matakai na sayen filaye da kuma yarjejeniyar sayen makamashi na gwamnati.

“Ana ɗaukar matakan tabbatar da cewa mun sayi filayen kuma zuwa shekarar 2027 ya kamata a ce mun yi bikin fara aikin gini,” in ji shi.

Dadkta Sogbadji ya ƙara da cewa ma’aikatar tana aiki cikin wa’adi na watanni shida domin faɗaɗa samun lantarki, inda take da niyyar samar wa kashi 90 cikin 1000 na ƙasar makamashi.

A watan Fabrairun shekarar 2025, Ghana ta karɓi baƙuncin tawagar bin ba’asin harkar nukiliyarta ta farko inda ƙwararru daga Pakistan da Turkiyya da Birtaniya da kuma Amurka, wadanda gwamnatin ta gayyata kuma kmafanin makamashin nukiliyar Ghana ya karɓi baƙuncinsu.

Tawagar ta yi nazari kan wuraren da ake son a gina tashoshin nukiliyar a kai, inda ta fi son Nsuban a lardin Yammacin ƙasar yayin da ta ɗauki Obotan a lardin Tsakiyar ƙasar a matsayin wuri na ko ta kwana, tana mai dubi kan yadda ake zaɓan wuri da sharruɗa da tattara bayanai.