Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Joint Task Force North West Operation FANSAN YAMMA sun ƙaddamar da wani gagarumin farmaki kan ƙungiyoyin ’yanta’adda da ’yanbindiga a Jihar Katsina, bayan sacewa da kashe tsohon Manjo Janar Rabe Abubakar.
An fara gudanar da wannan farmaki mai suna Operation CLEAN SWEEP III a ranar 14 ga watan Yuni, inda aka mayar da hankali kan Ƙaramar Hukumar Matazu da maƙwabtanta, wuraren da ƙungiyoyin masu aikata ta’addanci suka daɗe suna addabar al’umma.
A cewar rundunar sojin, an ƙaddamar da aikin ne a matsayin martani ga harin da ya yi sanadin mutuwar tsohon babban jami’in soja, wanda ’yanta’adda da ’yanbindiga suka sace shi tare da matarsa.
Mahukuntan sojin sun bayyana cewa manufar farmakin ita ce gano tare da kawar da waɗanda suka aikata wannan ta’asa, rusa hanyoyin sadarwa da cibiyoyin ayyukan masu laifi a yankin, tare da dawo da zaman lafiya a al’ummomin da abin ya shafa.
Tun bayan fara aikin, dakarun sun gudanar da sintiri na yaƙi, hare-haren da aka tsara bisa bayanan sirri, ayyukan kewaye da bincike, da kuma farmakin share maboyar masu laifi a wurare daban-daban da aka gano a yankin ayyukan rundunar.
Rundunar ta ce an samu nasarori masu yawa musamman a yankin tsaunukan Dikkawa da ƙauyukan da ke kewaye da su.
Dakarun sun kai samame tare da share maboyar da aka gano a yankunan Adua, Nasarawa da Karaduwa, inda aka binciki wurare da dama da ake zargin ’yanta’adda ke amfani da su.
A yayin waɗannan hare-hare, jami’an tsaro sun gano tare da lalata cibiyoyin ajiye kayan aiki da sauran wuraren tallafa wa ayyukan ’yanta’adda. Rundunar ta ce hakan zai ƙara raunana ƙarfin masu laifin wajen gudanar da ayyukansu a yankin.
Operation FANSAN YAMMA ta bayyana cewa ana gudanar da farmakin ne cikin haɗin gwiwa da sauran rassan jami’an tsaro, hukumomin tsaro daban-daban da kuma masu ruwa da tsaki na cikin gida, waɗanda gudunmawarsu ke taimakawa wajen inganta tsaro a jihar.
Rundunar ta sake tabbatar wa mazauna Matazu da ƙauyukan da ke maƙwabtaka cewa tana nan daram wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma masu bin doka, tare da hana ’yanta’adda da ’yanbindiga samun damar gudanar da ayyukansu cikin walwala a yankin.
Haka kuma, mahukuntan sojin sun yi kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai cikin lokaci domin taimakawa wajen gano tare da kama masu aikata laifuka, tare da tabbatar musu da cewa za a kiyaye sirrin duk wani bayani da aka bayar.
Rundunar ta ce za ta ci gaba da matsa lamba kan ’yanta’adda da ’yanbindiga har sai an cim ma dukkan manufofin wannan aiki.
Ana sa ran za a ci gaba da fitar da ƙarin bayanai yayin da farmakin ke ci gaba da gudana.







.jpeg?width=512&format=webp&quality=80)


