| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
An kashe aƙalla mutum 10 yayin da dakarun tsaron Guinea suka yi arangama da masu haƙar zinare
Gwamnatin ta masu zanfa-zangar sun kafa shinge a lokacin sintirin jami'an tsaro.
An kashe aƙalla mutum 10 yayin da dakarun tsaron Guinea suka yi arangama da masu haƙar zinare
An kase aƙalla mutum 10 yayin da dakarun tsaron Guinea suka yi arangama da masu haƙar zinare / Reuters (Wire)

Faɗa ya kaure tsakanin dakarun tsaro da masu haƙar zinare a arewa maso gabashin Guinea a wanna makon, inda ya yi silar kashe aƙalla mutum 10, in ji gwmanatin ƙasar ta Yammacin Afirka ranar Alhamis, yayin wani harin murƙushe haƙar ma’aidinai ba bisa ƙa’ida ba.

Tashin hankalin ya faru ne a gundumar Siguiri mai arzikin ma’adinai ranar Laraba, in ji wata sanarwar gwmanati, biyo bayan bayyana haramci na ranar 2 ga watan Nuwamba na haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a yankin inda aka tura sojoji daga baya.

Harbe-harben bindiga suna kaure inda aƙalla mutum 10 suka mutu, ciki har da ‘yan ƙasashen ƙetare biyar, kamar yadda gwmanatin ta bayyana.

Mutum goma sha uku, ciki har da dakarun tsaro, sun jikkata, in ji ta, tana mai ƙrawa da cewa gwmanatin ta gabatar da lamarin a ga masu gabatar da ƙara don “ƙra haske a kansa yanayin” da lamarin ya auku.

An kori dubbai

Tun lokacin da dokar haramta haƙar zinare ta fara aiki ne dakarun tsaro suka kori dubban ‘yan ƙasashen waje da suka zo aiki a mahaƙar ma’adinai na yankin.

Masu zanga-zanga suna kafa shinge a lokacin sintirin dakarun tsaro, in ji gwamnatin.

“Lamarin ya rikiɗe zuwa arangama,” in ji gwamnatin, tana mai cewa harbin bindia ya kaure ba tare da bayyana tushen harbin na farko ba.

Mazauna yankin sun shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa an girka jami’anbtsaro da yawa a wajen, inda mutane da yawa suka gaza ko kuma sun jin tsoron zuwa wajen da aka yi arangamar.

“Na ga gawarwaki a lokacin da lamarin ya lafa ɗan kaɗan,” kamar yadda wani shaida ya bayyana wa AFP, yana mai ƙrawa da cewa “an fasa shaguna tare da kwashe kayayyaki daga cikinsu.”

Wani shaidan kuma ya bayyana wa AFP cewa an ji wa mahaifinsa ciwo yayin aukuwar lamarin.

Aikin hana haƙar zinare ba bisa ƙ’ida ba ya haddasa kwararar mutane zuwa ƙasar Mali mai maƙwabtaka.

Gwmanatin ƙasar ta bayyana ranar lahadi cewa Mali ta karɓi kimanin mutum 160,000 da aka kora daga Guinea kuam ta bayyana damuwarta game da wani lamarin jinƙi na gaggawa.