| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Gwamnatin Kano tana bukatar rigakafin cutar mashaƙo miliyan tara daga gwamnatin tarayya
Masana lafiya sun yi kira ga iyaye da su riƙa kai yaransu asibiti da wuri idan suka ga alamomi kamar zazzabi, tari, ciwon maƙogwaro, kumburin wuya, ko bayyanar farin abu a makogwaro, kuma a guji cire ko yanke wannan abu a wuya a wajen wanzamai.
Gwamnatin Kano tana bukatar rigakafin cutar mashaƙo miliyan tara daga gwamnatin tarayya
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf / FB: Abba Kabir Yusuf

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa tana buƙatar alluran rigakafin cutar Mashaƙo (Diphtheria) guda miliyan tara daga Gwamnatin Tarayya domin gudanar da rigakafi na musamman ga al'ummar jihar, yayin da cutar ta mashaƙo ke bazuwa.

Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dokta Abubakar Labaran Yusuf, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da TRT Afirka Hausa kan matsayin cutar a jihar.

Kwamishinan ya bayyana cewa tun daga watan Disamba na shekarar 2022, Jihar Kano take fama da ɓullar cutar Mashako. A cewarsa, mutane 39,432 ne aka tunanin sun kamu da cutar, inda aka tabbatar da kamuwar mutane 32,581. Har ila yau, cutar ta yi sanadin mutuwar mutane 1,733 a faɗin jihar a tsawon wannan lokaci.

Me ke janya cutar mashako?

Dokta Abubakar Labaran ya bayyana cewa Mashako cuta ce da ƙwayar cuta ta bacteria ke haifarwa, kuma tana yaɗuwa cikin sauƙi ta hanyar shakar iska. Ya ƙara da cewa cutar tana saurin yaɗuwa a wuraren da ake samun taron jama'a, kamar masallatai, wuraren ɗaurin aure, kasuwanni, da tashoshin mota.

Gwamnatin jihar ta bayyana kasancewar waɗansu manyan ƙalubale da suka kawo tsaiko wajen yaƙi da cutar, wadanda suka haɗa da rashin damar gwamnatin jiha ta siyo alluran rigakafin Mashako kai-tsaye daga kasuwa, sai dai ta hanyar Gwamnatin Tarayya kaɗai, da samun yara da dama da ba a yi musu rigakafin cututtuka na yau da kullum ba a baya.

Wani ƙalubalen in ji Dokta Abubakar Labaran, shi ne jinkirin kai mara lafiya asibiti, “kai yara asibiti a makare bayan cutar ta riga ta lalata sassa masu muhimmanci a jiki kamar ƙoɗa, zuciya, ko sa zubar jini.”

Kwamishinan ya kuma yi gargaɗi kan dabi’ar da wasu mutanen suke yi ta yanke farin kurjin da ke fitowa a makogwaron yara ta hanyar amfani da wanzamai, wanda hakan ke janyo zubar jini da mutuwar yara nan-take.

Matakan yaƙi da cutar

Dokta Abubakar Labaran Yusuf ya ce gwamnatin Jihar ta Kano ta ɗauki wasu mataki domin ɗakile cutar da kawo ƙarshenta.

Matakan sun haɗa da kafa kwamiti na musamman wanda ya ƙunshi dukkan masu ruwa da tsaki a fannin lafiya da al'umma domin jagorantar yaƙi da cutar.

Sai kuma farfaɗo da cibiyoyin kula da masu cutar guda 44 a dukkan ƙananan hukumomin jihar tare da ba da magunguna da jiyya kyauta, in ji kwamishinan.

Ya ƙara da ce gwamnati ta sanya sarakuna da hakimai a ciki domin gudanar da gangamin wayar da kan al'umma a karkara da birni.

Kwamishinan ya kuma yi kira ga iyaye da su riƙa kai yaransu asibiti da wuri idan suka ga alamomi kamar zazzabi, tari, ciwon maƙogwaro, kumburin wuya, ko bayyanar farin abu a makogwaro, sannan ya gargaɗi jama'a da su ƙauce wa kwashe ko yanke wannan abu a wajen wanzamai.