| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
Jirgin yaƙin Amurka samfurin F-35 ya faɗi kusa da wani sansanin soji
An garzaya da matuƙin jirgin wani asibiti "domin duba lafiyarsa da kuma yi masa magani na raunukan da ya ji da ba sa barazana ga rayuwa," in ji jami'ai.
Jirgin yaƙin Amurka samfurin F-35 ya faɗi kusa da wani sansanin soji
Jami'ai na kashe wutar da ke cin wani jirgin yaƙin F-35 da ya faɗi kusa da titin sauƙar jirgin sama na sojin ƙasar da ke a San Diego, California

Wani jirgin yaƙin Amurka samfurin F-35 ya faɗi a kusa da wani sansanin soji a San Diego, amma matuƙin jirgin ya samu ya kuɓutar da kansa kafin jirgin ya kai ƙasa, a cewar jami’ai.

"An samu wani hatsarin jirgi da ya shafi wani jirgin sojojin ruwan Amurka [samfurin] F-35B a cikin harabar" filin jirargen saman sojin ruwa na Miramar da misalin ƙarfe 10:00 na safe (ƙarfe 1700 agogon GMT), kamar yadda wani mai magana da yawun sojin ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP.

"An fitar da matuƙin jirgin kuma an samo shi."

Wata sanarwar da aka fitar daga baya daga sansanin sojin ta ce an kai matuƙin jirgin wani asibiti "cikin wani yanayi na daidaito domin duba lafiyarsa da kuma yi masa magani na raunuka da ba sa barazana ga rayuwarsa."

Bidiyon da aka yayata a shafukan sada zumunta sun nuna hayaƙi na tashi sama daga jirgin saman, a yayin da aka tura ‘yan kwana-kwana su kashe wutar.

Filin jiragen sama sojin ruwan (MCAS) da ke Miramar sananne ne a faɗin duniya a matsayin inda ya taɓa kasancewa gida ga makarantar horas da matuƙan jiragen yaƙi na sojin ruwan Amurka inda ake horas da manyan matuƙan jirage, wanda ya yi suna a fim ɗin shekarar 1986 mai suna "Top Gun" inda Tom Cruise ya fito a matsayin tauraro.

Ko wane jirgin F-35B, wani samfuri na jirgin yaƙi mai tafiya cikin sirri babu ƙara da ke iya tashi sama kai tsaye da kuma sauƙa kai tsaye, kudinsa ya kai kimanin dala miliyan $109, in ji Lockheed Martin mai ƙera shi.

Rumbun Labarai
Wuta za ku je idan ba ku jefa ƙuri'a a zaɓen 'yan majalisa ba, in ji Trump ga 'yan Republican
Shekaru 25 bayan 9/11, Amurkawa na tsoron ta’addancin cikin gida fiye da barazanar hari daga waje
Turkiyya da kasashe 7 sun yaba wa Birtaniya kan hana kawo kaya daga haramtattun mazaunan Isra'ilawa
An samu sojojin Jamus da laifuka kusan 2,000 da suka shafi cin zarafi ciki har da lalata da yara
Koriya ta Arewa ta yi alƙawarin kafa rundunar sojin ruwa mai amfani da makaman nukiliya
Faɗaɗa Yarjejeniyar Makka: Me Bangladesh za ta iya kawo wa ƙawancen?
Kotu a Las Vegas ta samu tsohon jagoran 'yandaba Duane 'Keffe D' Davis da laifi a kisan Tupac Shakur
Cizon sauron da suka shiga Jamus ta jirgin sama ya kashe ma'aikatan filin jirgi biyu
Tsananin zafi ya yi ajalin mutane 15,800 a Jamus a bazarar bana
Shugaban hukumar leƙen asiri ta Rasha ya tabbatar da ganawa da Shugaban CIA a Moscow
Ambaliya da zaftarewar ƙasa a Nepal sun yi ajalin gommai da ɓatar da ɗaruruwa a kusa da iyakar China
Trump ya gabatar da yarjejeniyar shekaru 30 ta haɗin gwiwar nukiliyar Saudiyya ga Majalisar Amurka
Mummunar guguwa ta katse wutar lantarki a gidaje 26,000 a kudu maso-gabashin Faransa
An kama mutane da dama bayan zanga-zangar ƙyamar Musulunci a Amurka
Fitaccen tsohon ɗanwasan Brazil Roberto Carlos ya musulunta - Rahotanni
Fafaroma ya yi kira a kawo karshen cin zarafin da Isra'ila ke yi wa Falasdinawa a Gabar Yamma
CIA ta yi shakkar iƙirarin da Isra'ila ta yi kan shirin halaka Trump bayan taron NATO: rahoto
Za a fara shari'ar wanda ake zargi da hannu a kashe Tupac Shakur a Amurka
‘Yan Bangladesh akalla 16 sun mutu sakamakon gobara a masana'antar yin kujeru ta Saudiyya
Gobarar daji a jihar Washington ta Amurka ta tilasta wa dubban mutane tserewa