‘Yan ƙungiyar Lakurawa sun kashe mutane da dama tare da lalata ƙauyuka bakwai a hare-haren da suka kai a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Nijeriya, kamar yadda ‘yan sanda suka shaida wa AFP a ranar Alhamis.
Kakakin 'yan sandan jihar Kebbi Bashir Usman ya ce 'yan kungiyar Lakurawa sun kai hari a ƙauyukan da ke gundumar Bui a yankin arewa da misalin karfe 1:15 na rana a ranar Laraba.
Wani rahoton tsaro da AFP ta gani ya ce maharan sun kashe "mutanen ƙauye fiye da 30".
Usman ya shaida wa AFP cewa: "An kashe mutane da yawa yayin da mazauna Mamunu, Awasaka, Tungan Tsoho, Makangara, Kanzo, Gorun Naidal, da Dan Mai Ago suka yi gangami don tinkarar maharan."
Ya ƙara da cewa maharan sun kuma sace wasu shanu a cikin hare-haren. An aika 'yan sanda, sojoji da kuma 'yan sa-kai na yankin nan take zuwa wajen da abin ya faru.
Hare-haren sun faru ne kwanaki bayan da jihar ta karbi bakuncin bikin kamun kifi na Argungu da UNESCO ta saka a kundin tarihi na duniya, kimanin kilomita 60 (mil 38) daga yankin Arewa, inda aka kai hare-haren.
An zargi kungiyar Lakurawa da kai hare-hare da dama kan al'ummomi a arewacin jihar da kuma jihar Sokoto mai maƙwabtaka da ita.
Mambobin ƙungiyar suna kai hare-hare masu muni daga dazuzzukan da suke samun mafaka, suna satar dabbobi da kuma sanya "haraji" ga mazauna yankin.
Gwamnatin Nijeriya ta ce hare-haren sama da sojojin Amurka suka kai a ranar Kirsimeti a Sokoto sun shafi 'yan kungiyar da kuma gungun 'yan fashi.
Wasu masu bincike sun danganta kungiyar da kungiyar IS da ke yankin Sahel, wacce ke da ƙarfi a kasashen Nijar da Mali, duk da cewa wasu na tababar hakan.
Ayyukan ƙungiyar sun ƙara ta'azzara rashin tsaro a Nijeriya.
Ƙasar Afirka ta Yamma tana fama da rikicin da aka shafe fiye da shekaru 16 ana yi a arewa maso gabas, da kuma rikicin manoma da makiyaya a yankin arewa ta tsakiya.
Haka kuma tana fuskantar tashin hankali mai tsanani na 'yan-aware a kudu maso gabas da kuma sace-sacen mutane don neman fansa ya addabi arewa maso yamma.
Yanzu haka Nijeriya na neman tallafin fasaha da horo daga Amurka ga sojojinta da ke fafatawa da kungiyar bayan sake barkewar rikici da ya haifar da tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu.
Rundunar Sojojin Amurka ta Afirka ta ce ana sa ran sojoji 200 za a kai ƙsar.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce tashin hankalin da ke faruwa a wurin ya yi daidai da "muzguna" wa Kiristoci -- wani abu da bangaren masu tsananin kishin addini da siyasa na Amurka ya dade yana yarda da shi.
Gwamnatin Nijeriya da ƙwararru masu zaman kansu da dama sun ce Kiristoci da Musulmai duk suna fuskantar matsalolin tsaro a kasar.














